Ɓata gari sun Yashe Ɗakin ajiyar abinci a Abuja, sun kwashe komai - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Monday, October 26, 2020

Ɓata gari sun Yashe Ɗakin ajiyar abinci a Abuja, sun kwashe komai

 


Ɓata gari sun Yashe Ɗakin ajiyar abinci a Abuja, sun kwashe komai.


Wasu bata gari sun kai farmaki sashin masana’antu da ke yankin Idu, Abuja inda suka ɓalle ɗakin ajiyar kayayyaki.


Haka zalika bata garin sun far ma rumbun ajiya na hukumar NEMA, sannan suka yashe kayan abincin da aka ajiye a ciki.


 Lamarin ya afku ne a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba, yayinda matasa ke ta ɓarna a sassa daban-daban na kasar


Ɓata gari a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba, sun yashe wani rumbun ajiya mallakar hukumar bayar da agajin gaggawa ta tarayya (NEMA) a yankin Jabi adali Biu.


Har ila yau, ɓata garin sun kai farmaki rumbun ajiya na masana’antu masu zaman kansu a yankin Idu, babbar birnin tarayya, sun sace kayayyakin abinci.


A yayin mamayar, Matasan sun sace buhunhuna da dama na kayan abinci, shinkafa, kwalayen madara, galolin man gyada, abincin gwangwani, kwalayen taliya, da dai sauransu.


Ɓata garin sun sha karfin jami’an yan sanda a wajen, jaridar ThisDay ta ruwaito.


Mafi akasarin barayin sun zo ne da adaidaita sahu da babura domin cika su da kayan da suka sata.


Yankin Idu na dauke da masana’antu masu yawan gaske wadanda ke dauke da rumbun ajiya domin adana kayayyaki.


A gefe guda, gwamnonin jihohi 36 na Najeriya sun karyata boye kayan abincin tallafin COVID-19 da kungiyoyi masu zaman kansu suka samar don sassautawa talakawa radadin zaman gida lokacin kullen COVID-19.


Kungiyar manyan 'yan kasuwa da kamfanoni wadanda suka taru suka kira kansu da CACOVID, sun hada biliyon nairori don taimakon 'yan Najeriya a kan cutar Coronavirus, wacce tayi ajalin mutane a kalla 1,139, sannan ta shafi mutane 62,992.


Domin siyan DATA Ta MTN da take yin wata daya 1GB Kan 350 Yi magana ta WhatsApp https://wa.me/c/2348122225296

No comments:

Post a Comment