Nan ba da jimawa ba, Najeriya zata shiga jerin kasashen da suka cigaba a fanin kimiyya da fasahar zamani - Kashifu - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Saturday, October 24, 2020

Nan ba da jimawa ba, Najeriya zata shiga jerin kasashen da suka cigaba a fanin kimiyya da fasahar zamani - Kashifu


Nan ba da jimawa ba, Najeriya zata shiga jerin kasashen da suka cigaba a fanin kimiyya da fasahar zamani.


Najeriya Ta Dukufa Wajen Bunkasa Fannin Kasuwanci Da Fasahar Zamani -NITDA


Hukumar bunkasa fasahar sadarwar ta zamani NITDA, ta ce a shirye take ta bunkasa kasuwanci, musamman wajen amfani da kafofin yanar gizo a kasar, wanda mafi akasarin matasan kasar za su ci gajiya.


Shugaban hukumar Kashifu Inuwa Abdullahi, ya shaida hakan a wata tattaunawa ta musamman da Muryar Amurka akan matakai da suke dauka don ganin kasar ta bi sahun kasashen duniya a fanin kimiyya da fasahar zamanin a bangaren kasuwanci.


Hukumar mu ta zo da wani tsari da ake kira Strategic Roadmap na ya za’ayi a canja harkar fasahar zamani baki daya a kasar, don gogayya da kasashen da suka ci gaba a fadin duniya.


Muna da tsari da ke dauke da Taswirori guda hudu, wanda muka fara daga shekara ta 2016 zuwa shekara ta 2020, wanda ke nufin cewa karshen shekarar nan za’a kare wannan tsarin da muka yi.


"A ciki, mun fitar da bincike guda 7 da muke son mu aiwatar, wanda idan aka yi zai daura Najeriya akan harkar tattalin arziki na zamani wato "Digital Economy." Inji Kashifu 


Tsare-tsaren sun hada da Developmental Regulation, za’a kawo doka da zata bunkasa wannan harkar, dokar zata taimakawa ‘yan kasa su gane mai ya kamata suyi da fasashar zamani, hakan zai basu damar samun cigaba na tattalin arzikin su.


Kana a ciki mun zo da dokar da ake kira Nigeria Data Protection Regulation, doka ce wadda take tantance wane irin bayanai suka kamata mutane  su daura a Internet


Haka gwamnati ko wata hukuma idan zasu karbi bayani, wane irin suka kamata da wadanda basu kamataba, wannan tsarin da muka zo da shi ya bude ma mutanen hanyoyin ayyukan yi, a cikin kasa da shekara daya mun samu mutane kasa da dubu 2 da 700 da suka samu aikin yi.


A bangaren kasuwar wannan harkar a yanzu ta fi naira bilyan 2, sannan daga ciki muna zuwa da wasu tsare-tsare da zasu taimaka wajen bunkasa tattalin arziki, da kuma wadanda zasu taimaka wajen tabbatar da cewa an yi ayyuka dai-dai a gwamnatance.


Ko a kwanan nan akwai tsarin da muka fitar wanda 'yan kasa zasu ci gajiyar shi, wanda za su iya samun aiki a wata kasa kuma su gabatar da shi alhalin suna nan Najeriya wajen amfani da yanar gizo. 

Mun zo da wannan tsarin ne saboda mun ga kamar kasar Indiya a duniya itace ta mamaye wannan bangaren kasuwanci, sai muka ga ai Najeriya mun fi Indiya dama idan za’a yi.


Na farko, lokacin mu ya fi kusa da America da Turai a kan lokacin Indiya, na biyu Najeriya mun fi mutanen da suka iya turanci, saboda yanzu kasar Indiya ma wadanda suka iya turanci suna raguwa, saboda haka muka fitar da tsarin ya za’a yi Najeriya ta mori wannan tsari.


Akwai kuma tsarin Digital Capacity Building, saboda harkokin duk fasahar zamani sai mutum na da ilimi. akwai horaswa da muke yiwa mutane daban-daban, wanda a cikin shekara 1, daga watan Agustar shekarar 2019 zuwa Agustar shekarar 2020 da mu ke ciki hukumar NITDA ya horar da ‘yan kasa kusan dubu 40.


No comments:

Post a Comment