Yan bindiga sama da 100 sun kai hari Zamfara, sun hallaka mutane 20
Yan bindiga sun hallaka akalla mutane 22 a garin Tungar Kwana dake karamar hukumar Talata-Mafara ta jihar Zamfara daren Talata, 20 ga watan Oktoba, 2020, Jaridar The Punch ta ruwaito.
Wani dan garin, Malam Ahmed Mohammed ya bayyanawa wakilin Punch cewa yan bindiga sama da 100 sun kai hari kauyen misalin karfe 11 na dare kuma suka fara harbe-harbe.
"Mutane ashirin da biyu, wanda ya hada da mata da yara aka kashe lokaci guda, yayinda wasu suka gudu cikin daji."
Mohammed ya kara da cewa mutane da dama sun jiggata sakamakon harbi kuma an garzaya da su asibiti domin jinya.
A cewarsa, yan bindigan sun yi awon gaba da dabbobi da yawa. "Sun kwashe mana shanu, tumakai, da akuyoyi da kuma kayan abinci," Inji Mohammed.
Ya ce mutane sun gudu daga garin saboda tsoron dawowan yan bindigan saboda sun dade suna kai hari.
kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya ce "Hukumar yan sanda ta tabbatar da kisan mutane 20 amma ba mutane 22 ba.
" Shehu ya ce yan bindigan sun kai harin ne saboda mutanen garin sun baiwa jami'an tsaro bayani kansu wanda yayi sanadiyar kisan da yawa cikinsu. Ya ce hukumar yan sanda ta tura jami'anta Domin damke yan bindigan.
A bangare guda, Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta shari'ar Musulunci a Najeriya (NSCIA), Alh Muhammad Sa'ad Abubakar, ya ayyana ranar Juma'a a matsayin ranar addu'a ta musamman ga Najeriya.
Sarkin ya ce umurci Musulman Najeriya su yi addu'a bisa rikicin da yayi sanadiyar asarar rayuka da dukiya a Legas, Benin da wasu jihohi.
Jami'an tsaro sun kashe aƙalla Mutane 20 tare da jikkata fiye da 50 a zanga-Zangar EndSARS a Legas
https://www.arewagist.com.ng/2020/10/jamian-tsaro-sun-kashe-fiye-da-mutane.html
No comments:
Post a Comment