Masu zanga-zanga sun ragargaza Fadar Sarkin Legas, sun cinna wa gidan mahaifiyar Gwamnan Legas wuta
Duk da dokar-ta-baci da aka kafa a Lagos, mafusatan masu zanga-zangar EndSARS sun fito sun ci gaba da kona muhimman wurare a cikin Lagos.
A safiyar Laraba an ragargaza Fadar Oba na Lagos, Eilwanu Akiolu, kuma aka rika jidar kayayyaki masu muhimmanci da tsada ana guduwa da su.
Wani bidiyo da aka nuna, an ga matasa na gudu bayan sun fito daga fadar, kowa ya rungumo kayan sata. An ga wani a gaba dauke da sandar mulkin Babban Basaraken na Lagos.
Hadimin Sarki Rilwani ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an kutsa cikin fadar an saci kaya masu yawa. Kuma an ragargaza wasu sassa na cikin fadar. Deoye Olumegbon, wanda shi ma Dan sarauta ne, ya ce an yi babbar barna a fadar.
Yadda Sojoji SuKa Ceci Sarkin Lagos Daga Hannun Masu Zanga-zanga
Hadimin sa ya ce yayin da masu zanga-zangar suka gama ragargaza ofishin ‘yan sanda na Ebute Ero, sai suka yi wa Fadar Oba na Lagos tsinke. Ganin yadda aka kewaye gidan ana kwasar kaya, sai aka kira sojoji domin su kai masa dauki.
“Nan take aka turo sojoji cike da motoci biyar, suka kutsa suka ceto shi.”
Eilwanu Akiolu dai tsohon babban jami’in dan sanda ne, kuma dan jam’iyyar APC ne rikakke.
A zaben 2015 ya yi barazanar korar baki daga Lagos, wadanda ba ‘yan asalin jihar ba, matsawar ba su zabi Akinwunmi Ambode da Buhari a lokacin zabe ba.
An ƙona Gidan Mahaifiyar Gwamnan Lagos, Sanwo-Olu
Wani rahoto kuma ya tabbatar da cewa masu zanga-zanga sun ragargaza gidan mahaifiyar Gwamnan Lagos da ke unguwar Surulere, kan titin Akerele Street, a Lagos.
Wani jami’i ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa an ragargaza gidan sai dai bai san ko da me da me aka sace ba.
Zanga-zangar ta yi muni bayan kashe masu zanga-zanga da sojoji su ka yi a Lekki da tsakar daren Talata.
No comments:
Post a Comment