Zanga-Zangar EndSARS ta haifar da asarar sama da naira biliyan 400 a Legas - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Thursday, October 22, 2020

Zanga-Zangar EndSARS ta haifar da asarar sama da naira biliyan 400 a Legas



Zanga-Zangar EndSARS ta haifar da asarar sama da naira biliyan 400 a Legas


Gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa ta yi asarar kimanin sama da dalar Amurka biliyan É—aya sakamakon rikicin da ya É“arke a jihar, biyo bayan zanga-zangar EndSars da ake yi.


A hira da BBC, Shugaban Cibiyar Kasuwanci Ta Legas, Muda Yusuf, ya ce duk da cewa ba a gama tattara alƙaluma kan ƙiyasin asarar da wannan tarzoma ta jawo ba, amma an yi asarar sama da dalar Amurka biliyan ɗaya, kimanin kuɗin Najeriya naira biliyan 400 kenan.


A ranar Laraba ne dai tarzomar da aka yi a jihar ta Legas ɗin tafi ƙamari inda aka lalata gidaje da ofisoshi da masana'antu da wuraren aiki.


Duk da jami'an tsaron da aka jibge a jihar domin shawo kan tarzomar, an ɗauki lokaci mai tsawo ana ƙone-ƙone a cikin jihar.


"An shafe kusan mako biyu da fara tagayyara tattalin arziƙin Legas da na Najeriya sakamakon wannan zanga-zangar, ganin cewa Legas ita ce cibiyar kasuwanci ta Najeriya," in ji shi.


A cewarsa, idan aka samu tsaiko na tattalin arziƙi a Legas, tasirin da abin zai yi ga Najeriya yana da yawa, kuma zai ɗauki lokaci mai tsawo kafin a farfaɗo.


"Gwamnati ta yi asara, kamfanoni masu zaman kansu sun yi asara, haka masu zuba jari, an yi asarar sama da ƙadarori 100 kuma ba wai ƙanana ba,", a cewarsa. Kadarorin dai sun haɗa da ofisoshi da kamfanoni da masana'antu da sauransu.


Jami'an tsaro sun kashe aÆ™alla Mutane 20 tare da jikkata fiye da 50 a zanga-Zangar EndSARS a Legas 

https://www.arewagist.com.ng/2020/10/jamian-tsaro-sun-kashe-fiye-da-mutane.html


Wane tasiri wannan asarar za tayi ga tattalin arziƙin Legas da Najeriya


Mista Muda Yusuf ya bayyana cewa wannan asarar ta mayar da hannun agogo baya ta fuskar ci gaban da ƙasar ke samu bayan ƙasar ta fara farfaɗowa daga asarar da aka samu a lokacin annobar korona.


"An samu raguwar tattalin arziƙi da kashi 6.1 a watanni shidan farko na wannan shekara, yanzu kuma ga wata sabuwar girgiza an sake samu, wannan yasa ake ƙara mayar da hannun agogo baya.


"An samu koma baya a ɓangaren zuba jari da farfaɗo da tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi."


A cewarsa, sanadiyar lalata wasu kamfanoni da masana'antu, hakan zai jawo mutane da dama su rasa ayyukansu, ya kuma ce akwai kamfanoni da dama da cikin shekara É—aya ko biyu ba za su iya farfaÉ—owa ba.


"Kadarorin kamfanoni da dama da aka lalata da ke ƙarƙashin tsarin inshora, wanda hakan zai ƙara matsin lamba ga kamfanonin bayar da inshora.


Masu zanga-zanga sun ragargaza Fadar Sarkin Legas, sun cinna wa gidan mahaifiyar Gwamnan Legas wuta

https://www.arewagist.com.ng/2020/10/masu-zanga-zanga-sun-ragargaza-fadar.html


Girman asarar da aka yi a Legas

A tattaunawar da BBC tayi da Muda Yusuf, ya bayyana cewa an lalata da kuma ƙona wurare a jihar ta Legas sama da 100.


Ga kaɗan daga cikin wuraren da muka tattaro da aka lalata ko kuma ƙonawa.


Hedikwatar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, NPA


Gidan Oba na Legas


Gidan talabijin na TVC


Gidan mahaifiyar Gwamna Sanwo-Olu


Tashar mota ta Oyingbo


Otel din Orientel


Ofishin hukumar Road Safety da VIO


Babbar Kotun da ke Igbosere


Manyan kantunan sayar da kayayyaki na Shoprite da Spar


Ofishin jaridar The Nation


Wasu daga cikin ofisoshin 'yan sandan da aka lalata


Ofishin 'yan sanda na Idimu


Igando


Layeni


Denton


Ilenbe Hausa


Ajah


Akwai kuma ofishin 'yan sanda na Amukoko


Akwai ofishin rusashshiyar rundunar SARS a Ajegunle.


An Bankawa hedikwatar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa Wuta a Legas

https://www.arewagist.com.ng/2020/10/an-bankawa-hedikwatar-hukumar-kula-da.html


Wane mataki aka ɗauka na cike giɓin asarar da aka tafka a Legas?


Mista Muda Yusuf ya bayyana cewa a halin yanzu babu wani mataki a ƙasa da za a ce an ɗauka na cike giɓin irin wannan asarar ganin cewa har yanzu mutane na cikin ruɗani da kaɗuwa duba da irin girman asarar da aka tafka.


Ya ce kamfanonin da suke da inshora ne kaɗai a yanzu za su ɗan samu sauƙi wurin farfadowa, amma waɗanda ba su da inshora hakan na nufin sai dai su haƙura ko kuma su san yadda za suyi su farfaɗo da kansu.


Ya ce a ɓangaren gwamnati, sake gina waɗannan kadarorin a wurin ta yana da wahala matuƙa duba yadda tattalin arziƙi ke tafiya da kuma yanayin samun harajinta ya ragu.


Ya ce da kudin da aka yi asara, ya isa a yi wa mutane ayyuka da suka shafi asibitoci da tituna da gidaje.


An cinna wa motocin haya wuta a tashar Oyingbo da ke Legas

https://www.arewagist.com.ng/2020/10/an-cinna-wa-motocin-haya-wuta-tashar.html

No comments:

Post a Comment