Ba za mu lamunta ba wanda ya ɓoye bayan EndSARS ya karya doka da cin zarafin ƴan Najeriya ba – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnati ba za ta sa ido ta bari wasu na boyewa bayan wannan zanga-zangar #EndSARS ba suna gallaza wa mutanen da basu ji ba, basu gani ba azaba ba.
Ya roki masu zanga-zangar #EndSARS su hakura hakanan, cewa gwamnati ta saurare su kuma za ta aiwatar da bukatun su.
Daga nan sai ya mika jajen sa ga ƴan sandan da suka rasa rayukan su a wajen wannan gwagwarmaya.
” Ina kira ga kasashe makwabtan mu da sauran kasashen duniya da su rika bin diddigi su nemi bayanan gaskiya game da abin da ke faruwa a kasar nan kafin su fadi ra’ayoyin su. Su daina biye wa kafafen sada zumunta na yanar gizo.
Ina mika jaje na ga ƴan sandan da suka rasa rayukan su a wannan gwagwarmaya da kuma wadanda aka rasa rayukan su a dalilin zanga-zangar #EndSARS.
Daga nan sai shugaba Buhari yayi kira ga masu zanga-zangar #EndSARS da su janye sannan su dakatar da zanga-zangar, yana mai cewa gwamnati ta saurare su kuma zata yi kokarin biya musu bukatun su.
Shugaba Buhari yayi jawabi da Karfe 7 na yammacin Alhamins ga ƴan Najeriya, bayan an shafe makonni biyu a na zanga-zangar #EndSARS a musamman jihohin yankin kudancin Najeriya.
No comments:
Post a Comment