Dalilin da yasa ƴan Najeriya ke gaba-gaba wajen kasuwancin Kuɗaɗen Internet Cryptocurrencies - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Tuesday, March 2, 2021

Dalilin da yasa ƴan Najeriya ke gaba-gaba wajen kasuwancin Kuɗaɗen Internet Cryptocurrencies


 Dalilin da yasa yan Najeriya ke gaba-gaba wajen kasuwancin kudaden intanet Cryptocurrencies


Kasuwancin kudaden intanet a Najeriya na kara samun karbuwa sama da ko ina a duniya, wanda hakan ke nuna karancin Gamsuwar da ake da ita a irin kasuwancin da aka saba da su da zuba hannayen jari, kamar yadda rahoton Ijeoma Ndukwe ya bayyana.


Tola Fadugbagbe ya bayyana yadda ya koma Legas shekara 10 baya tare da sa ran gobensa za ta zama mai kyau.


Maimakon samun gobe mai kyau, sai ya kare a samun ayyuka kanana da ba a samun kudi sosai - wannan shi ne labarin mafi yawan matasan Najeriya da ke kokarin samun rayuwa mai kyau.


Abubuwa ba su daidaita ba har sai a 2016, lokacin da yaga tallan Bitcoin kuma abin ya ja hankalinsa, daga nan ne ya fara harkarsa ta kudaden intanet.


Na fara ne da bincike mai zurfu," in ji Mista Fadugbagbe ya shaida wa BBC.


"Ina share sa'o'i masu yawa ina kallon bidiyo a YouTube ina kuma karanta rubuce-rubuce a kan Bitcoin. Ba ni da kudade da zan fara kasuwancin kamar yadda ya kamata, don haka na fara da dala 100 zuwa 200."


Wannan shawarar da ya yanke ce ta sauya rayuwarsa baki daya.




Tola Fadugbagbe

Mai harkar kuɗin intanet

Babu ɗan Najeriyar da zai fara harkar kuɗin intanet da zai so ya daina. Babbar dama ce."


Lokacin da muke tattaunawa, Mista Fadugbagbe ya ce a yanzu yana gudanar da kasuwanci a kullum tare da koyawa masu zuba hannun jari, ya ce yana da kudin intanet da suka kai sama da dalar Amurka 200,000 mallakarsa.


Kwanan nan zan koma gidana na kaina, wanda nake ginawa yanzu. Ina da gona katuwa duk ta dalilin wannan kudaden intanet," ya yi murmushi.


"Babu dan Najeriyan da zai fara kasuwancin kudaden intanet ya daina ba karamar dama ba ce."


Labarin nasarar Mista Fadugagbe ya ja hankulan milyoyin 'yan Najeriya kan harkar kudaden intanet kamar su Bitcoin Ethereum da Sauran su.


Wani bincike da aka yi a intanet a 2020, ya bayyana cewa kashi 32 cikin 100 na 'yan Najeriya na amfani da wannan harka ta kudaden intanet - kaso mafi yawa da ake da shi a wata kasa daya kenan a duniya.


Kasuwancin kuɗin intanet a Najeriya a 2020

Ana kasuwancin kuɗin intanet na 1.1M Dollar a duk wata a Najeriya


dala miliyan 65 da ake kasuwancin kuɗin Internet duk wata a manhajar Paxful


dala 100 ake kashewa kusan a kan kowane ciniki


dala 215 ake kashewa kusan a kan kowane ciniki a Amurka


Hasashe ya nuna cewa cikin kasashe 10 da ake wannan kasuwancin a 2020, Najeriya ce a matsayi na uku bayan Amurka da Rasha, inda ake juya sama da dalar Amurka miliyan 400.


Duk da cewa Najeriya ta fita daga cikin durkushewar tattalin arziki karo na biyu cikin kasa da shekara biyar, amma matsalar tattalin arzikin da ake kai har yanzu tana nan, wanda ya mayar da kasuwanci kudaden intanet zabi mai kyau ga 'yan kasar da dama.


Babban Bankin Najeriya ya rage darajar naira da kashi 24 cikin dari a bara. Akwai kuma fargabar cewa za ta kara karyewa da kashi 10 a wannan shekarar.


A gefe daya kuma farashin abubuwa na ci gaba da tashi, yayin da kayan abinci suka yi tas gwauron zaɓi tun a Watan Yulin 2008



Michael Ugwu

Mai harkar kuɗin intanet

Na samu naira amma na yi asarar dalar Amurka. A lokacin ne na gane cewa buge-bugen da muke akwai koma baya."


Lokacin da Micheal Ugwu, wanda yake da wani kamfanin jarida a Legas, ya sayar da kasar da yake da ita a 2018, ya gano cewa akwai bukatar sake zuba hannun jari a wasu harkokin na daban.


Duk da cewa yadda yake samun kudi ya karu, amma ya samu koma baya a ta bangaren dala saboda karya darajar dalar Amurka.


"Ina samun naira sosai amma ina asarar dala. Shi ne lokacin da bige-bigenmu na komawa baya. To a lokacin ne na fara neman Bitcoins."


"Amma komawa wannan harkar ta ceto rayuwa ta," in ji shi.


'Kyautatuwar harkokin bankin'

Matarsa Onyeka ta fara wannan kasuwanci ne lokacin da bankin ke cire mata kudade masu yawa a yayin aika kudi daga Najeriya zuwa Burtaniya.


"Ba maganar samun kudi ba ce. magana ce ta yadda za a kyautata harkokin banki. Dole kayi a jiya a inda darajar kudinka ba zata rube ba."


Karya darajar naira da karancin dalar Amurka ya sanya mutane neman yadda za su samu kudi a hannunsu


Duk da cewa ana samun kudi da irinsu Bitcoin amma ana da yakinin wata rana zai durkushe.


Haramta kudaden intanet

A wata sanarwa da aka saki a ranar 7 ga watan Fabrairu, ta ruwaito bukatar da ake da ita na tsare dukiyoyin jama'a daga tsoron da ake na cewa wasu da ba a sani ba, suna gudanar da wani kasuwanci haramtacce".


Tun daga nan mutane da dama suke korafin ana rufe musu asusu saboda alaka da kudaden intanet.


Manajan Mista Fadugbagbe ya kira shi ya ce za a kulle asusunsa matukar bai cire kudadensa ba cikin kwana guda.

Amma fa ba kowa ne ya samu irin wannan sa'ar ba.


Wani shaida ya ce an rufe asusunsa makonni biyu baya kuma da kudade masu yawa ciki.


'Kada a rufe shi baki daya'

Wannan ce hanyar da ake amfani da kudaden intanet gabanin samar kasuwar bai daya a Najeriya.


Mista Ugwu ya ji mutane da yawa na maganar kudin intanet da neman komawa kasashen da suke bari ana wannan kasuwanci ba tare da matsawa ba kamar su Ghana da Rwanda da kuma Saliyo.


Damuwar da hukumomi ke da ita idan ana maganar kudaden intanet ita ce, ana amfani da su ne ta hanyoyin da ba su dace ba.


Tsohon mataimakin gwamnan Babban Bankin Najeriya Kingsley Moghalu, yana ganin cewa gwara kasar ta rungumi tsarin maimakon rufe shi baki daya - musamman tun da yana taimakawa mutane da yawa suna samun na kansu lokacin da ake cikin matsin tattalin arziki".


'Na fi amincewa da kudaden intanet sama da hannun jari'

'Yan Najeriya na ganin kudaden intanet a matsayin wata hanya ta kaucewa rashin samun kudaden ketare.


"Akwai iyakoki da yawa kan abin da za mu iya da wanda ba za mu iya ba da kudaden ketare," In ji Nena Nwachuku da ke aiki da wani kamfani.


"Yana yi wa 'yan Najeriya da dama sauki yin amfani da kudaden intanet a matsayin wata hanya ta zuba hannun jari."


An kulle asusun wadanda suka shirya zanga-zangar EndSars, su kuma sai suka nemi a rika amfani da kudaden intanet


Yunkurin kame masu zanga-zangar a hannu ta hanyar rufe asusun bankinsu ya janyo karuwar amfani da kudin intanet, abin da ya sanya Bitcoin ya rika tashe a Twitter.


Misis Nwachukwu ta ce wannan ya share musu hanyar bude sabon asusu da kuma karuwar hada-hadar da ake yi da kudaden.


Da yawa sun ta nuna fushinsu kan manufofin gwamnatin Najeriya da yadda tattalin arzikinta ya samu koma baya.



No comments:

Post a Comment