Menene Blockchain Technology ? - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Tuesday, March 9, 2021

Menene Blockchain Technology ?

 


Menene Blockchain Technology ?

Ana kirkirar Crypto Currencies, akan Block Chain Technology, shi kuma block chain Technology tsari ne na Database, duk wanda yasan me ake kira da database toh zai yi saurin fara hasaso wannan kimiyyar ta Block Chain.


Database wuri ne ko tsari ne da ake ajiye bayanai, da tattara su wuri guda ko a rarrabe, tare da canza su ko gyara su a lokacin da ake bukata.


Tsarin database yana da yawa, yafi guda 40 a bangaren ilimin Computer, akwai Distributed database, akwai Relational database, akwai Centralized, akwai decentralized, akwai Cloud da sauran su.


Toh shi Block Chain Technology yana kan tsarin Decentralized distributed ledger ne, sai dai tsarin sa yasha ban ban da asalin tsarin database ta wasu wurare, shi Block Chain Technology tsari ne wanda ba'a iya canza bayanan dake cikin sa da zaran an shigar, kuma ba'a iya sace shi, ko hacking din sa ko ayi masa kutse saboda tsaron da aka saka masa.


Har yau an gagara samun wani ko wasu kwararrun hackers da suka iya hacking din Block Chain Technology, ba'a samu ba, hatta wadanda suka fi kowa kwarewa a harkar Internet da suke kasar Switzerland da Japan da Uruguay sun sadakar cewa ba zasu iya hacking din komai ba dake kan Block Chain Technology, wato ginin Mahadi ka ture kenan.


Shi Blockchain Technology baya karban komai sai dai dai da tsarin sa, toh idan ya karba kuma babu wanda zai iya dakatar dashi har wanda ya kirkiro tsarin.


Haka zai yi ta tafiya duniya tana amfana dashi Koda masu shi sun mutu ko sun watsar dashi.


Misali, koda wanda ya kirkiro Bitcoin bazai iya dakatar dashi ba, sai dai ya hakura.


Haka kuma tsarin Block Chain Technology yana iya gano Wanda yayi kokarin shiga da bayanan da ba dai-dai ba, kuma ya dakatar da mutum na har abada daga shiga tsarin domin 'dora Coin ko wani information.


Sannan ba'a iya kwace shi zuwa hannun mutum guda, saboda an gina Blockchain Technology ne akan tsaron da wani 'dan Adam ba zai iya canza shi ba.


Kuma baya karkashin kulawar wata kasa ko wata gwamnati ko wani mutum, wannan shine babban dalilin da yasa gwamnatocin kasashe ke yaki da Block Chain Technology, saboda basu da iko dashi.


Toh sai dai asalin tsarin Block Chain Technology ba anyi shine saboda harkar kudin Intenet kadai ba.


A'a anyi shi saboda duk wata harkar ajiye bayanai ta Online ne a duniya, sai dai harkar kudin Crypto Currency ta sanya mutane da dama basu san cewa blockchain Technology bai tsaya akan harkokin kudi kadai ba.


Menene Crypto currency?

Kamar yadda aka sani kalmar Crypto asalin ta kalmar Girkawa ce (Greek Word), tana nufi "Secret" ko "Hidden", abin nufi "Sirri" ko "É“oyayyen abu", daga nan aka samo kalmar Crypto da ma'anar ta, dalilin da yasa aka bawa kudin internet wannan suna shine saboda yadda aka shirya tsarin kimiyyar gudanar dashi, akan wani tsari da ake ce wa "Blockchain Technology", ko "Kimiyyar da take jere akan tsari hawa-hawa kamar bulo".

Crypto Currency kudi ne dake internet, wanda aka fara mu'amala dashi daga 2009 zuwa yanzu.


Sai dai, kafin a fara wannan harkar Crypto currency a yau, tun da dadewa, wuraren 1980s, masana harkokin internet suke ganin ya dace duniya ta samar ma kanta da harkokin kudaden da ba'a iya ganin su, kuma ba'a iya taba su.


Saboda cigaba da amfani da kudaden takarda yana 'kara karya tattallin arziki duniya.


Ta yadda gwamnatoci suke kashe kudade masu yawa wurin buga su, da kashe kudade masu yawa wurin kula dasu idan sun yage ko sun 'koke ko sun lalace, sannan ana saurin sace su da gano inda suke da wanda yake dasu.


Wannan yana daga cikin ababen da suka sa manyan masana ganin a kawo karshen wannan matsalar.


Tun daga lokacin da aka fito da tsarin transfer din kudi ta waya, daga Account din mutum na banki zuwa wani banki masana suka tabbatar da cewa tsarin Block Chain Technology zai yi nasara.


Har wa yau, tun shekarun baya masu kokarin kwato 'yancin 'dan Adam suna cewa ya kamata ace a yanzu mutane sun samu "Financial Freedom" wato " 'Yancin gashin kai ta bangaren harkokin kudi", ba sai sun jira wata kasa ko wata gwamnati ta amince da kudi kasa ba.


Suna cewa saka bakin gwamnati cikin harkar kudi yana danne cibagan duniya da walwalar mutane.


A shekarar 1985 wani Baturen kasar America masanin harkar internet yayi yunkurin samar kudin Intenet mai kama da Crypto Currency na yanzu, sai dai kasar Amurka ta kama shi, ta daure shi, daga bisani aka yi zargin ta hallakar dashi.


A 1997 wani dan kasar Japan ya sake irin wannan yunkurin na samar da kudin Intenet amma kasar Japan ta kama shi, haka dai abun ya cigaba da tafiya tsakanin masu neman "Financial Freedom" da gwamnatocin kasashe.


A shekara ta 2008 wani masanin harkar internet kuma dan rajin neman Financial Freedom a duniya, wanda aka ce sunan sa "Satoshi Nakamoto", yayi nasarar kera kudin Intenet, kuma ya saka masa suna "Bitcoin".


Bayan ya kammala aikin a 2008, sai a 2009 ya qaddamar dashi, wanda shine yayi nasara a karon farko a tarihin duniya da har aka gagara dakatar dashi.


Sai dai ance Satoshi Nakamoto ya gina aikin sa ne akan wanda 'dan kasar Japan din nan ya faro.


Har yanzu ba'a san fuskar Satoshi Nakamoto ba, sai dai bincike ya nuna cewa suna ne irin na 'yan kasar Japan.


Shi ya Samar da Kudin farko "Bitcoin", an saka masa sunan ne saboda an gina lissafi na'urar juyawa kudin ne da lissafin Computer na salon Algorithm, wato shi Algorithm asalin wanda ya kirkiro wannan lissafin da Computer take kai wani babban Malamin Musulunci ne, sunan sa "Imam Jabir Bin Hayyan Al-Khawarizmi", shine Turawa suka boye sunan sa domin kada duniya tasan Musulmi ne suka kawo wannan tsarin lissafin na Computer.


Tsarin lissafin algorithm akan Computer yana bugawa ne da 'digo ko "Bit".


Toh daga nan suka saka sunan kudin Crypto currency na farko da "Bitcoin", shi Bitcoin a Ranar (08-03-2021) yana Naira miliyan 25,000,000 a kudin Nigeriya.


Amma a farkon lokacin da aka kirkiro sa a 2009 bashi da daraja, bayan shekaru 10 ya tashi daga Naira goma ya koma Naira miliyan 24 ko wane daya, misali: wanda ya sayi Bitcoin guda dari a 2009 a yau Duk guda daya Naira Milyan 25


Bitcoin ba shi kadai ne Crypto Currency ba, shi Bitcoin 'daya ne daga cikin kudaden Internet, shine na farko, shine babba dan haka yafi kowane Coin tsada.

Misali:

Idan aka ce maka akwai kudaden Takarda a duniya (Fiat Currency) a duniya da yawa, toh kudin Nigeriya (Naira) ba itace kadai kudin da ake amfani da ita a duniya ba.


Akwai Riyal, akwai Dollar, akwai Cefa, akwai Ghana Cedi, akwai Pound, akwai Yuro da sauran su.


Toh haka ma Crypto currencies suke, akwai su da yawa sun fi dubu uku akan Block Chain Technology na duniya, misali, akwai:

1. Bitcoin.

2. Etherium.

3. Litecoin.

4. Binance (BNB).

5. Doge coins.

6. Tron (TRX).

7. ADA, Cardano.

8. Steem, Hive, XRP, HOT, Smartkey da CLASSIC COIN



No comments:

Post a Comment