.
A rubutun da ya gabata muna bayani ne game da ABUBUWAN DA SUKA ZAMA WAJIBI KA AIKATA A MATSAYINKA NA DAN KASA MUSULMI A HARKAR ZABE.
.
● ka fita da wuri ka kada kuri'arka da zarar lokacin kadawar yayi.
.
Ka kyautata mu'amalar ka da Jami'an zabe wajen neman sanin yanda zaben zai gudana. Ka mutunta sirrin sauran masu kada kuri'a.
.
● Ka tabbatar kana da katinka na dindindin na Zabe tare da kai duk sanda zaka tafi rumfar Zabe domin kada kuri'a. Kada ka bada wani uzuri cewa ka manta dashi a gida ko kuma ka batar kuma sannan ka bukaci kada kuri'a. Jami'an zabe suna da damar da zasu hana ka kada kuri'a. Idan ka batar da katinka na Zabe, ya kamata kabi matakan da suka dace wajen sanar da Jami'an zabe kafin ranar Zabe.
.
Kafin ka kada kuri'a, kabi a hankali ka tabbatar ka dangwala yatsanka a gurbin da aka tanada dake nuna alamar jam'iyyar dan takarar da kake so ka zaba a jikin takardar kada kuri'a domin ba za'a baka wata takardar kada kuri'a ba idan kayi kuskure.
.
● Ka tabbatar ba wanda yaga wanda ka zaba, shi zai sanya ya zama ka kada kuri'a ta cikin Sirri. Wanda zaka zaba ya zama ba wanda ya sani daga kai sai ALLAH. Domin a matsayinka na musulmi ya kamata kayi Zabe tsakaninka da ALLAH.
.
● Ka jira har sai an kirga kuri'u kuma ka kiyaye sakamakon da jami'an zabe suka fadi kuma suka lika.
.
● Ka sani don dan takarar ka yayi nasara a rumfar zabenka ko gudumawar da ka bashi ke nuna dan takarar ka ne ya lashe wannan zaben ba. Haka kuma idan dan takarar ka ya fadi a rumfar zabenka ko gudumawar da ka bashi ke nuna dan takarar ka bazai iya lashe zaben ba. Ko wani dan takara yana da inda yafi tarin magoya baya da kuma inda 'Yan hamayan su suke da tarin magoya baya.
.
● Ka tabbatar an samu ingantaccen zabe ta hanyar bin dokoki da tsare-tsaren zabe, ta haka ne zamu san duk wanda yaci ya ci ne bisa ga yardar ALLAH. Saboda ALLAH shi baya goyon bayan rashin gaskiya da zalunci kamar magudin zabe da tursasawar wanda suka fadi akan jama'a.
.
● Idan kaga wani abu ya tafi ba daidai ba a ranakun zabe kana da 'Yanci a matsayinka na dan kasa ka kai kara ma hukumar Zabe ko kuma wasu amintattun kungiyoyin da bana siyasa ba da suke aiki da hukumar Zabe don tabbatar da samun ingantattun zabuka.
.
Acikin Alqur'ani mai girma ALLAH (SWT) Yace:
.
Ù‚ُÙ„ِ اللَّÙ‡ُÙ…َّ Ù…َالِÙƒَ الْÙ…ُÙ„ْÙƒِ تُؤْتِÙŠ الْÙ…ُÙ„ْÙƒَ Ù…َÙ† تَØ´َاءُ Ùˆَتَنزِعُ الْÙ…ُÙ„ْÙƒَ Ù…ِÙ…َّÙ† تَØ´َاءُ Ùˆَتُعِزُّ Ù…َÙ† تَØ´َاءُ ÙˆَتُØ°ِÙ„ُّ Ù…َÙ† تَØ´َاءُ ۖ بِÙŠَدِÙƒَ الْØ®َÙŠْرُ ۖ Ø¥ِÙ†َّÙƒَ عَÙ„َÙ‰ٰ ÙƒُÙ„ِّ Ø´َÙŠْØ¡ٍ Ù‚َدِيرٌ
.
“Ka ce: "Yã ALLAH Mamallakin mulki, Kanã bayar da mulki ga wanda Kake so, Kanã zãre mulki daga wanda Kake so, kuma Kanã buwãyar da wanda Kake so, kuma Kanã Æ™asÆ™antar da wanda Kake so, ga hannunKa alhẽri yake. Lalle ne Kai, a kan kõwane abu, Mai Ä©kon yi ne." [Q-3;26]
.
● Akwai Lambobin waya a karshen wannan rubutu domin kai rahoton duk wani abunda ke tafiya ba daidai ba kamar zuwan kayan zabe a makare, ko kuma rashin jami'an tsaro, kuntatawa, kwacen akwatin zabe, lalacewar na'urar tantance katin zabe. Da zarar ka lura da haka to ka kai rahoto yayin da zaben ke gudana domin hukumar Zabe ta magance matsalar acikin lokaci.
.
#OurVoteOurPower.
#CommunityLifeProject(CLP)
#Nigeria2019.
No comments:
Post a Comment