Yadda zaka samu ATM CARD dinka bayan ya maqale a ATM MACHINE. - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Saturday, February 23, 2019

Yadda zaka samu ATM CARD dinka bayan ya maqale a ATM MACHINE.

Yadda zaka samu ATM CARD dinka bayan ya maqale a ATM MACHINE.

Maqalekar ATM a jikin machine wani abu ne mara dadi musamman idan hakan ya faru a ranakun hutu, wato ranakun da ba'a aiki.

Idan ATM dinka ya maqale a cikin machine, kanada zabi biyu:

Na farko: YIN SABO A BANKIN KA
Wannan yana nufi ka sake yin sabon ATM a bankin ka. Zaka iya yin hakan ne idan ATM dinka ya maqale a banki wanda ba naka ba kuma bakason shan wahala kawai sai kaje bankin ka suyi maka sabo. Amma koda ba'a bankin ka bane ya maqale idan ka shiga wannan bankin domin yi musu korafi, zasu ce maka kaje bankin ka.

A duk lokacinda ATM ya maqale a banki alhal ATM din ba na wannan bankin bane, sukan dauka ne sukan asalin bankin wannan ATM din. Saboda haka samun ATM dinka a bankin ka abune mai sauki.

Na biyu: ZUWA WURIN CUSTOMER CARE
Customer care sune wadanda ke sauraron korafin customers dinsu. Misali idan ATM dinka na First bank ne kuma ya makale a ATM na First bank, to kawai zaka shiga bankin ne ka samu wannan customer care din zai baka wata takarda (form) domin cikewa. Sannan zasu buqaci wani abu da zasu tabbatar ATM din naka ne kamar ID CARD da sauransu.

Bayan an kammala wannan zasu baka ATM dinka.

A duk lokacinda mutum ya samu kanshi a cikin wannan hali yanada zabi cikin wadannan hanyoyi biyu.

Zaku iya yi mana tsokaci (comment)  akan ra'ayoyinku game da wannan shafi, sai mun jiku.

Abu Abdirrahman Kaltungo
CEO Arewagist.com.ng
Info@arewagist.com.ng
23rd February, 2019

No comments:

Post a Comment