[[Ka Karanta]] Sabbin abubuwa dake tattare da WhatsApp version 2.19.98 - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Saturday, April 20, 2019

[[Ka Karanta]] Sabbin abubuwa dake tattare da WhatsApp version 2.19.98

Da farko ya kamata kowa yasan ta yaya zai duba version na WhatsApp da yake amfani dashi, domin kowanne yanada sauye-sauye da yake dashi, shi wannan na ambata a sama shine na karshe wato zuwa yanzu babu wani a gaban shi.

Domin sanin version da kake amfani dashi, bayan ka hau WhatsApp dinka a saman hannun dama zakaga wasu layuka 3 a jere daga sama zuwa kasa sai ka danna su, bayan ka danna su zakaga setting sai ka shiga.

Bayan zai nuna maka options, sai ka zabi na kusa da karshe wato HELP, bayan ka shiga nan ma zakaga wasu options sai ka zabi APP INFO, to anan ne zakaga version da kake amfani dashi.

SABBIN ABUBUWAN VERSION 2.19.98
1. SHARING
Kawai zaka iya yin sharing zuwaga mutane 5 ne ko group 5.

A baya munsan cewa kana da damar yin sharing ga dukkan groups  da kake dasu ko dukkan contacts dinka, wato babu iya, amma bayan an fidda version din da ta gabata sai suka takaita zuwa groups 20 kawai ko contacts 20, amma fitan wannan version din sun sake rage shi zuwa groups 5 kacal.

2. KALLON YOUTUBE VIDEO
Kafin fitan wannan version da nake magana akai, idan aka turo maka youtube link to dole sai kabi wannan link din ya kai ka YouTube kafin ka kalla, amma yanzu da zaran an turo maka YouTube link kawai zaka danna hoton ne daga nan video naka zai playing maka a cikin WhatsApp dinka, basai kaje YouTube ba.

3. GOGE CHAT HISTORY CIKIN SAUKI
Kafin wannan version ya fita, idan kanason goge chat da kayi sai ka shiga kowanne group daya bayan daya ka clearing chat din, koko kaje ta kan wayarka ka shiga setting>app>whatsapl>clear data.

Yanzu an kawo saukin yin hakan, kawai ka shiga wurin wancan layi ukun, za nuna maka options sai ka zabi setting, sai ka zabi chat bayan nan a karse zakaga chat history sai ka shiga, zakaga abubuwa 4 sai ka zabi wanda kake so ko clear ko delete.

4. TAMBAYAR REPORT NA ACCOUNT
Domin sanin wannan sai ka shiga wurin wancan layuka ukun sai ka shiga account, wato zabin farko, bayan ka shiga a can kusa da karshe zakaga wannan request account information zai ka shiga.

5. YIN KIRA DA MUTANE DA YAWA
Wannan yana nan kamar conference call ne, idan kuma WhatsApp call da wani, a can sama ta hannun dama zakaga alamar adding contact sai ka shiga.

Zamu cigaba da kawo muku abubuwanda suka shafi fasaha.

Kada a manta a ajiye tsokaci (comment) domin samun karfin gwuiwa.

Abu Abdirrahman Kaltungo
CEO Arewagist.com.ng
Info@arewagist.com.ng
20th April, 2019

1 comment: