~Ko Kasan an sanya Ranar da za'a fara Printing na Jamb Slip Examination
~Hukumar Jamb ta dage Jarabawar Mock data Sanya ranar 23rd
~Yau (Laraba) Hukumar Jamb ta Kara bude Portal din ta
Hukumar Shirya Jarabawar Share fagen shiga Jami'a (wato Jamb a takaice) ta sanya ranar 1 ga watan April a matsayin ranar da za'a gudanar da Jarabawar Mock aduk fadin kasar, hakan yazo ne sakamakon Zabukan da za'a canja a wasu Jihohi guda 6 ranar 23 ga watan March wanda yayi daidai da ranar da za'a gudanar da Jarabawar Mock din kamar yadda Hukumar ta jamb ta sanya tun a farko, Saidai Canja zaben a wasu Jihohin ya tilasta wa Hukumar ta Jamb dage ranar yin Mock din daga 23rd March zuwa 1st April, 2019.
Saboda haka yanzu Jarabawar Mock za'a yita ne a ranar 1st April 2019. Hukumar tana kara sanar da dalibai cewa duk wanda ya riga yayi Printing na Mock Examination Slip dinshi to ba sai ya kara yin wani Printing din ba, Saboda babu wani abunda aka canja illa kawai ranar da za'ayi Mock din.
Haka kuma Hukumar ta Jamb ta sanya ranar 2 ga watan April a matsayin ranar da za'a fara Printing na Jarabawar ta Jamb, dan haka take jan kunnen kowanne dalibi da ya tabbatar yayi Printing din Jamb Examination Slip din nashi kafin ranar da zaiyi Jarabawar, kuma kowanne dalibi zai iya yin Printing din Slip din nashi a ko ina ne ba dole sai a CBT centre ba.
Hakanan Hukumar ta bayyana ranar 11 ga watan April cewa ranar ne za'a fara gudanar da babbar Jarabawar ta Jamb wacce za'a share sati daya anayi. Dangane da sake bude Portal kuma, mai magana da yawun Hukumar ta Jamb Dr. Fabian Benjamin yace "Hukumar ta Jamb ta bude Portal din ta jiya Laraba (13th March, 2019) dan kammala Rajistar ta Jarabawar Jamb.
Mr. Benjamin yace akwai Kimanin Dalibai dubu Arba'in da daya da sittin da uku (41,063) da suka bude Profile na Jamb ko DE, kuma suka siya ePINS amma kuma basu samu damar kammala Rajistar ba har aka rufe, to dan haka an bude Portal din daga jiya (13th March, 2019) zasu iya zuwa su karasa yin Rajistar su, kuma za'a kara rufe portal din ne a ranar Juma'a 15th March, 2019. Sannan karku manta bawai ana kara siyar da Jamb ko DE din bane, a'a wannan dama ne na daliban da suka riga suka siya jamb ko DE din ne amma basu samu damar yin Rajistar ba har aka rufe.
Dan haka Arewa SOF tana kara Shawar tar dalibai da su kara dagewa da karatu kafin ranar Jarabawar da zata kazance 11th April 2019, da fatar Allah Ubangiji ya bawa Kowa Sa'a, Ameeen.
Daga arewagist.com.ng
Daga arewagist.com.ng
No comments:
Post a Comment