Najeriya za ta sallami matasan dake cin moriyar tsarin N-Power su 500,000 - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Saturday, June 20, 2020

Najeriya za ta sallami matasan dake cin moriyar tsarin N-Power su 500,000

Najeriya za ta sallami matasan dake cin moriyar tsarin N-Power su 500,000

Ministar walwala da jin dadin al'umma, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa za'a sallami matasan dake cin gajiyar tsarin N-Power da aka dauka a shekarar 2016 wannan watan na Yuni, 2020.

Haka zalika za'a sallami wadanda aka dauka a 2018 a watan Yuli, 2020.

Shirin N-Power ya dauki matasa 500,000; karon farko an debi mutane 200,000 a Satumba 2016, sannan 300,000 a watan Agustan, 2018.

A lokacin da aka daukesu aiki, an bayyana musu cewa watanni 24 za suyi, amma matasa 200,000 na farko da aka dauka sun kwashe sama da watanni 40

A wani jawabi, Hajiya Sadiya Farouq ta ce gwamnatin tarayya ta fara shirin mayar da su wani shirin aikin hannu.

Tace: "Mun kaddamar da mayar da matasan diban farko da na biyu cikin wasu shirye-shiryen aikin hannu da gwamnati ta shirya tare da hadin kan wasu kamfanoni masu zaman kansu domin daukan matasan aiki.."

"Gwamnatin tarayya za ta cigaba da fadada shirin (N-Power) kuma yanzu zamu fara daukan sabbin matasa."

"Saboda haka, ma'aikatar na sanar da cewa za a sallami yan diban farko a ranar 30 ga Yuni, 2020 yayinda za a sallami Yan diba na biyu 31 ga Yuli, 2020."

Ma'aikatar ta ce za'a fara sabon dauka ne daga ranar 26 ga Yuli, 2020.

Za'a bude shafin yanar gizon rijista daga ranar 26 ga Yuni, 2020 domin masu bukata su nema.

N-Power shiri ne da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samar a shekarar 2016 karkashin ofishin jin dadin al'umma.

An samar da shirin ne domin rage yawan matasa marasa aikin yi a Najeriya da kuma rage talauci.


Shirin N-Power ya dauki matasa 500,000; karon farko an debi mutane 200,000 a Satumba 2016, sannan 300,000 a watan Agustan, 2018.

A lokacin da aka daukesu aiki, an bayyana musu cewa watanni 24 za suyi amma matasa 200,000 na farko da aka dauka sun kwashe sama da watanni 40



No comments:

Post a Comment