Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB?
Kashi Na 6
( 19-03-2019)
•Shin Ban iya Computer Bane?
•Shin Ban iya Karatun Bane?
•Mecece Matsalar?
Amsar Wannan Tambayar Tana Kunshe Ne a Abunda ka iya Hararowa Kai da kanka kokuma Wani wanda Yafahimci Hakikanin Matsalar ka.
Kungiyar Asof. Tadamu Matukar Damuwa Wajen Ganin Yawan Daliban Arewa Dasuke Faduwa
Jarrabawar JAMB,
Dayawa Daga Cikin Su da Asof. Ta zanta Dasu wasu Sunyi Jarrabawar JAMB so Biyu wasu So Uku wani Ma da Asof. Ta Tattauna Dashi So biyar Yayi JAMB beci Ba!
a ina Matsalar Take?
•>Matsala Ta Goma
•Rashin Samun Nutsuwa a lokacin yin jarrabawar:-
Kamar yadda kowa yasani cewa babu wani abu dazakayishi cikin rashin nutsuwa kuma yay kyau, don haka nutsuwa tana daya daga cikin abubuwan da ake bukata a lokacin yin wannan jarrabawa
Saboda Dalibai da dama suna rasa nutsuwarsu a lokacin wannan jarrabawar saboda dalilai kala daban-daban
Daga cikinsu kamar yadda ASOF tayi bayanai a baya akwai zuwa da wani abun wanda JAMB ta haramta shiga dakin jarrabawa dashi kamar Agogo, Calculator, Jaka, Waya, ATM card, Abin hawa, dadai sauransu.
Shawarwari akan wannan matsalar
1- yana dakyau kafin Dalibi yashiga dakin wannan jarrabawar yatabbatar cewa yaci abinci, saboda rashin cin abinci yana taka muhimmiyar rawa fagen rashin samun nutsuwa a lokacin wannan jarrawa
2-kada kajeka/kijeki wajen jarrabawar da daya daga cikin abubuwan da hukumar tahana shiga dakin jarrabawar dasu, saboda idan kaje dasu dole saidai ka ajiyesu a waje, kuma idan ka ajiyesu a waje inda babu tsaro zaka dinga tunaninsu, wanda hakan zai hanaka kayi jarrabawarka a nutse
3-ka/ki kiyayi zuwa da abin hawa gurin jarrabawar saboda akwai barayi, kuma tunanin ko bazaka fito kasameshiba saiya hanaka nutsuwa
3-kada ka/kiji tsoron jarrabawar a lokacin da ka/kika shiga dakin jarrabawar kunutsu sosai, ku fahimci tambayar, saboda fahimtar tambaya rabin amsane.
•>Matsala Ta Goma Sha Daya
•Rashin samun hanyoyin da zakuji bayanai/Labarai akan Jarrabawar:-
A yanzu haka mafiya yawan Daliban dasuka fito daga kauyuka, dakuma kadan Daga cikin Daliban dake birane suna fama da wannan matsalar ta rashin samun bayanai akan wannan jarrabawar wanda hakan babbar matsalace
Akwai wasu Daga cikin Dalibai masu karanta wannan program dazasuce meyasa wannan yazamo matsala to akwai dalilai.
Ta hanyoyin samun bayananne zaka fahimcima mecece jarrabawar jamb din, ya akeyinta, yaya tambayoyinta suke, meyake sawa a fadi jarrabawar, wadanda hanyoyi za'abi domin magance matsalolin da dai sauransu.
•Shawarwari Akan Wannan Matsalar:-
1•Yana Da kyau Dalibi Ya mallaki waya ko Computer wacce zaidinga duba meyake faruwa ko kuma a wanne hali wannan jarrabawar take
2•Yana da Kyau Daliban da basu iya wayaba ko computer, su mallaki RADIO domin jin labaran yadda ake ciki a wannan hukuma
3• Yakamata Dalibi yasami wani daga cikin masana a unguwarsu ko agarinsu yazame masa jagora a abubuwan da suka shige masa duhu
4• Idan baka cikin Group dinmu na ASOF JAMB GROUP kayi kokari kayi magana da admin din group din domin yasakaka.
*.* Matsala Ta Goma Sha Biyu
>Abubuwa/Ayyukan Rayuwa Sunyi maka Yawa:-
Abubuwa sukan iya yiwa Dalibi yawa wanda harzai rasa me mazaiyi, musammanma Daliban dasuke da hakkin ciyarda wasu, ma'ana Dalibai masu iyali kenan,
Masu wannan nauyi akansu, samun lokacin yin karatu dakuma duba bayanai akan wannan jarrabawar yanayi musu wuya saboda koyaushe suna tunanin ya za'ai su ciyarda iyalinsu, su tufatar dasu, su biya musu kudin makaranta, da dai sauran bukatu nayau da kullum
Saboda hakane wannan jarrabawar take zuwa musu da tsauri.
Shawarwari Akan Wannan Matsalar:-
1•To iyalai dai babu yanda zakai dasu, saboda haka yanada kyau ace koda minti 30ne kana warewa domin kadanyi karatu bayan kadawo gida, kada kace wai kagaji bazakayiba, a'a kadan taba komai kankantarsa zaiyi maka amfani
2•Saboda rashin lokacin yin amfani da waya ko kwamfuta, yanada kyau ace ko Radioce kadinga kunnawa domin jin yadda ake ciki gameda wannan jarrabawa.
3 *.* Sannan kada katauyewa iyalanka hakkinsu saboda zakayi jarrabawa.
4 *.* Dagewa da Addu'a tareda tawassuli da ciyarwa dakeyiwa iyalanka domin Allah yataimakeka kaci wannan jarrabawa.
Marubuci:- Miftahu Ahmad Panda.
(Mataimaki na Musamman Ga Secretary General na Asof).
Zamuci Gaba insha Allah.
Daga shafin arewagist.com.ng
No comments:
Post a Comment