Yana cikin sunnonin da aka manta da su yin addua a tahiyar karshe kafin yin sallama.
1-Daga Abdillahi Bn Mas'ud رضي الله عنه yana cewa:
Lallai Manzon Allah ﷺ ya koya mana tahiya sannan yace akarshe:
*(Sannan ka zabi adduar da so kayi a bayan Tahiya)*.
@رواه مسلم
Yin addua bayan Tahiya ta karshe mustahabbine kai tsaye,adduar da tazo daga Annabi Muhammad ﷺ ce ko kuma wadda ka tsarace da kanka,amma yin wadda tabbata daga Manzon Allah ﷺ tafi dacewa.
2-Manzon Allah ﷺ yace:
(Idan dayanku ya gama Tahiyarsa ta karshe,to ya nemi tsarin Allah daga abubuwa guda hudu:-
*-Daga Azabar wutar jannama*
*-Daga Azabar qabari*
*-Daga fitinar yaruwa da mutuwa*
*-Daga Sharrin Masihid Dujal)*.
@صحيح مسلم (588).
3-Daga Aliyu Bn Abi Dalib رضي الله عنه yace:
Manzon Allah ﷺ ya kasance abinda yake fada akarshen Tahiyarsa kafin sallama shine:
*(اللهمَّ ! اغفرْ لي ما قدَّمتُ وما أخَّرتُ.وما أسررتُ وما أعلنتُ ,وما أسرفتُ.وما أنت أعلمُ به مِنِّي .أنت المُقدِّمُ وأنت المُؤخِّرُ لا إله إلا أنتَ ))*
@صحيح مسلم (771)
4-Manzon Allah ﷺ ya shiga Masallaci sai ga wani mutum ya gama sallarsa yana tahiya sai yake cewa a karshen Tahiyarsa:
"اللَّهمَّ إنِّي أسألُكَ يا اللَّهُ الأحدُ الصَّمدُ الَّذي لم يلِد ولم يولَد ولم يكن لهُ كُفوًا أحدٌ أن تغفرَ لي ذنوبي إنَّكَ أنتَ الغفورُ الرَّحيمُ"
Sai Manzon Allah ﷺ yace:
*(Hakika an gafarta masa, Hakika an gafarta masa, Hakika an gafarta masa)*.
@صححه الألباني في صحيح أبي داود(985)
5-Abubakar Saddiq رضي الله عنه yana cewa:
"Nace da Annabi ﷺ
Ya Manzon Allah ﷺ ka koya min adduar da zai riqa yi acikin sallata,sai yace kace:
*(اللهم إني ظلَمتُ نفسي ظُلمًا كثيرًا،ولا يغفرُ الذنوبَ إلا أنت، فاغفِرْ لي من عِندِك مغفرًة،
إنك أنت الغفورُ الرحيمُ)*
@متفق عليه(7387-2705)
Yin addua acikin sallah abune mai falala amma anfi so ayi alokacin sujada da kuma bayan tahiya ta karshe kafin sallama,kuma wannan shine abinda Manzon Allah ﷺ ya kwadaitar.
Daga cikin akwai wannan adduar a tahiyar karshe
*(اللهم إني أعوذ بك من عذاب جهنم، ومن عذاب القبر، ومن فتنة المحيا والممات، ومن فتنة المسيح الدجال)*
Allah ne mafi sani.
Daga arewagist.com.ng
20th March, 2019.
No comments:
Post a Comment