*LABARAI A TAKAICE*
*YA KAMATA GWAMNATIN BUHARI TA YI TSAYIN DAKA WAJEN CAFKE MASU HALLAKA MUTANE-ZAUREN TATTAUNAR ADDINI*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*Zauren tattaunawar addinin musulmi da kirista na Najeriya ya bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tsayin dakar kamo duk masu hannu wajen zubar da jinin jama’a ba tare da hakkin shari’a ba don a hukunta su. Zauren wanda ya kammala taron wuni uku,ya ce lokacin yin uzuri ga gwamnatin ya wuce, don haka ta dage wajen kamo miyagun irin don yin adalci ga ‘yan kasa da a ka cutar.*
*A matsayin zauren na addini, ya ce ya dace ne ya rika magana cikin sara da duba bakin gatari, amma ga wannan lamari na masu kashe-kashe, lokaci ya yi da za a fuskanci gwamnati da bukatar daukar matakin ba sani ba sabo. Wannan zauren dai na karkashin jagorancin sarkin musulmi Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar da shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya Reverend Samson Supo Ayokunle.*
*Lamuran da ke damun ‘yan Najeriya baya ga ta’addancin ‘yan Boko Haram, akwai ‘yan fashi da makami,’yan bindiga da masu satar mutane. Kazalika rikicin kabilanci da kan juye na addini ma kan kawo matsala da sabani tsaknin al’ummar Najeriya mai yawan kabilu,akidu da talauci.*
*KU JE KU TANADI DOKA DON SANYA RUNDUNAR KU TA AMOTEKUN BISA KA’IDA-SAKAMAKON TARON OSINBAJO GA GWAMNONIN YANKIN YARBAWA*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*Yanzu dai rundunar nan ta tsaro da gwamnonin yankin kudu maso yamma mai akasarin kabilar Yarbawa ka iya cigaba da aiki bayan cimma matsaya da gwamnonin su ka yi da fadar Aso Rock. Taron dai wanda mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya jagoranta, ya yanke matsayar gwamnonin su koma jihohin su da tsara doka a majalisun su da zata ba da kariya don aiyukan rundunar da za ta zama tamkar ta ‘yan sintiri ko banga.*
*Batun kafa rundunar ta AMOTEKUN ya jawo muhawara mai zafi musamman daga al’ummar arewacin Najeriya da ke ganin tamkar yankin na Yarbawa na neman ware kan sa ne a kaikaice daga sauran sassan kasar. Shugaban kungiyar gwamnonin yankin kudu maso yamma gwamna Rotimi Akeredolu na Ondo ya ce an umurce su su koma don tsara dokar rundunar ta AMOTEKUN.*
*Gabanin taron da gwamnonin su ka bukaci yi da gwamnatin taraiya, Akeredolu ya ce ba abun da zai sanya fasa aikin rundunar. Dattijon arewa Alhaji Awaisu Giwa Kuta ya nuna takaicin ba da damar gudanar da rundunar da ya ce hakan zai iya kawo rabuwar kan ‘yan Najeriya. Za a jira sabuwar yiwuwar sabuwar sanarwa daga ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami kan AMOTEKUN da gabanin yanzu ya ce ta saba tanadin tsarin mulkin Najeriya.*
*ZA A GUDANAR DA SAKE ZABE A MAZABAR ESSIEN UDIM A JIHAR AKWA IBOM BA TARE DA APC MAI MULKI BA*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*Hukumar zaben Najeriya za ta gudanar da sake zabe a mazabar Essien Udim ta jihar Akwa Ibom a asabar din nan amma ba tare da shigar dan takarar jam’iyyar APC ba. In za a tuna Sanata Godswill Akpabio ya shigar da kara bayan faduwa zaben mazabar sakamakon nasarar da dan takarar PDP Chris Ekpenyong ya samu.*
*Kotun koli ce ta yanke hukuncin komawa a sake zaben. Tuni dama Akpabio ya ce ya fi son kujerar babban ministan Neja Delta da shugaba Buhari ya nada shi a kan komawa zabe. APC ta musanya Akpabio da Emem Ekperkpe amma duk da haka ta janye daga zaben da zargin hukumar zabe ba za ta yi ma ta adalci ba.*
*KUWAIT TA KIRA JAKADAN IRAN DON NUNA BACIN RAI KAN ZARGIN DA IRAN TA YI MA TA NA HANNU A KASHE JANAR SOLEIMANI*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*Kasar Kuwait ta gaiyaci jakadan Iran don nuna bacin rai kan zargin da Iran din ta yi ma ta cewa an yi amfani da daya daga cibiyoyin sojan ta na sama wajen kai hari da ya hallaka kwamandan Iran din Janar Qassim Soleimani a filin saukar jirage na Bagadaza.*
*Mataimakin ministan wajen Kuwait Khaled Al-Jarallah ya nuna mamakin Kuwait ga zargin da Iran din ta yi na hannun ta a hallaka Soleimani. In za a tuna shugaba Donald Trump ya gargadi Iran da gujewa kai wa sansanonin Amurka hari, don in ta yi hakan, Amurka za ta kai hari kan muhimman sassan Iran 52.*
*Ibrahim Baba Suleiman*
*Jibwis Media & Publicity*
*media@jibwisnigeria.org*
*29-Jumada-ul-awwal-1441*
*25-January*2020*

No comments:
Post a Comment