Anyi zanga-zanga saboda rusau a Kasuwannin Kano - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Monday, July 20, 2020

Anyi zanga-zanga saboda rusau a Kasuwannin Kano

zanga-zanga ta É“arke saboda rusau a Kasuwannin Kano

Ƴan tireda a kasuwar Sabongari sun nuna rashin amincewarsu da abin da suka kira a matsayin zalunci yayin da Hukumar Kula da Sufuri ta Kano KAROTA ta rushe musu rumfuna da shaguna.

Kwanaki uku da suka gabata ne Hukumar KAROTA ta yi rusau a wasu manyan kasuwanni na jihar Kano inda ta rushe fiye da shaguna 500 da ke wuraren da suka saɓa ƙa'ida a kan tituna.

A yau Litinin, Æ´an kasuwa da wasu al'ummar gari suka yi zanga-zanga ta nuna bacin rai dangane da wannan lamari da wasunsu ke kira a matsayin toshe musu hanyar cin abinci.


A wani faifan bidiyo da jaridar Daily Trust ta wallafa a shafinta na Twitter, ya hasko yadda wasu matasa ke zanga-zanga a bakin Kasuwar Singer daura da Kasuwar Sabon Gari.


Rahotanni sun bayyana cewa, an yi É—an takaitaccen rikici tsakanin jami'an 'yan sanda da kuma wasu daga masu kasa kaya a gefen tituna a bakin kasuwar Sabon Gari.

Taƙaddamar ta auku ne a yayin da 'yan kasuwar ke gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadin matakin da Gwamnatin Kano ta ɗauka na haramta kasa kaya a gefen titin kasuwar.

Kwanaki uku da suka gabata ne gidan Rediyon Freedom ya ruwaito cewa, Hukumar KAROTA ta sanar da kammala duk wani shiri na kai simame wuraren da 'yan kasuwa ke kasa a kan tituna da wuraren da basu dace ba.

Shugaban Hukumar KAROTA, Alhaji Baffa Babba Dan Agundi, shi ne ya bayyana hakan a yayin da ya kai ziyarar gani da ido wuraren da aiki zai biyo takansu tun a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli.

A yayin da yake zantawa da manema labarai, Dan Agundi ya ce akwai fiye da shaguna dubu biyar da aka bari kara zube a gefen tituna da bakin kasuwanni a birnin Kano da kewaye.

Daga cikin kasuwannin da shugaban KAROTA ya wassafa sun haÉ—ar da ta Sabuwar Tasha, Kwanar Ungogo, Unguwar Nassarawa, Yankin Masana'antu da kuma ta Sabon Gari.


No comments:

Post a Comment