Harin da aka kaiwa Zulum a Baga alama ce ta muma bamu tsira ba - Gwamnoni - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Tuesday, August 4, 2020

Harin da aka kaiwa Zulum a Baga alama ce ta muma bamu tsira ba - Gwamnoni

Harin da aka kaiwa Zulum a Baga alama ce ta muma bamu tsira ba - Gwamnoni

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce farmakin da gungun maharan da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka kaiwa tawagar gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum a garin Baga, alama ce dake nuna cewar su kansu gwamnoni basu tsira daga barazanar kungiyar ta Boko Haram ba.

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriyar kuma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ne ya fitar da sanarwar hadin gwiwar ga manema labarai, bayan taron da suka yi a ranar litinin a Abuja.

Taron gwamnonin da ya maida hankali kan sha’anin tsaro, ya koka kan yadda lamurra ke kara tabarbarewa a sassan Najeriya, duk da kokarin gwamnati na kawo karshen matsalar.

Ranar lahadin nan da ta gabata yayin karbar bakuncin gwamnonin Jigawa da Kebbi a Maiduguri, gwamna Babagana Zulum ya jadadda cewar, akwai wadanda ke yiwa gwamnati zagon kasa ga kokarinta na murkushe ta’addanci, matsalar da yace ba za ta bari a kawo karshen matsalar da yankin arewa maso gabshin kasar ke ciki ba.

A wani labarin kuma mai alaka da wannan, yau Talata shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da manyan hafsoshin tsaron kasar da sauran masu ruwa da tsaki a Abuja, inda ya Nuna musu fushinsa Kan matsalar tsaro da take Kara taɓarɓarewa

No comments:

Post a Comment