Gwamnatin jahar Borno ta janye dokar tirsa sa zaman gida dole, biyo bayan Samun ga garumar nasara Kan yaki da cutar Coronaviros a jahar.
Mataimakin gwamnan jahar Alh Umar kadafur ne yabayyana haka cikin wata sanarwa da aka fitar jiya laraba a birnin maiduguri.
Ya ce an janye dokar tirsa da zaman gidan ne domin nazar tar halin da ake ciki, amma Kuma Gwamnati za ta mayar da dokar idan akaga annobar cutar za tayi kamari.
Ya ce an wajabta yin amfani da amawalin rufe Baki da hanci, ya yin da aka umarci daukacin Ma'aikatan Gwamnati da sarakunan gargajiya tare da shugabannin addinai Dana al'umma su tabbatar suna bin ka'idojin da aka shimfida na samar da tazara alokacin ibada ko taron jama'a.
Mataimakin gwamnan ya Kara da cewa mutane guda ashin ne kadai aka sahhalewa halartar biki ko taron suna ko na jana'izar.
Sannan Ma'aikatan dake Kan matakin albashin na daya zuwa na goma Sha biyu zasu cigaba da yin aiki daga gida
No comments:
Post a Comment