Buhari ya karbi maganin Coronaviros na kasar daga hannun Shugaban kasar Guinea Bissau
Mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban Kasar Guinea Bissau Alhaji Umaro Sissoco Embaló, a fadar mulki ta Aso rock dake babban birnin tarayya Abuja.
A hukumance Shugaban kasar Guinea Bissau Malam Umar Sissoco, ya mika maganin cutar Coronavirus na gargajiyar na kasar Madagascar ga shugaban Nigeria Muhammadu
yace Buhari.
Buhari ya ce "Lallai ni nace a kawo mana maganin gargajiyar kasar Madagascar, kuma an kawo, amma mun sa masu ilimi suna duba maganin yanzu haka, idan an kammala dubawan kuma an tabbatar da babu wata matsala, to daga nan zan umarci mutanen kasa ta su fara amfani dashi".
Shugaban na Kasar Guinea Bissau ya kara da cewa; "Na zo Nigeria ne domin na nemi shawarar Uba a gare ni, akan hanyoyin yaki da cin hanci da rashawa bayan naci zabe, wannan shine dalilin zuwa wurin ka Baba". ~inji shugaban Umar Sissoco.
Mai magana da yawun shugaba Buhari Malam Garba Shehu ya rawaito wannan labarin.
No comments:
Post a Comment