Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya saki miliyan N285 ga Kwamitin Kula da Tallafin Kudi na COVID-19 da za a yi amfani dashi don magancewa Al'umma radadin zaman gida.
Gwamna ganduje ya ce zai ba da cikakkiyar damar rarraba kayan tallafi ga gidaje sama da 300, 000 wadanda aka yi niyya a cikin jihar Kano.
Shugaban Kwamitin, Muhammad Yahuza Bello ne ya sanar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati ranar Laraba.
Ya ce ya yin da Kwamitin ya kashe miliyan 100 wajen kashe kudaden a kashi na farko na rarraba kayan aikin, ana sa ran yin amfani da miliyan N170 don kammala kashi na biyu na ayyukan.
Malam Bello wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero Kano (BUK), ya ce Ganduje ya kuma umarci Kwamitin daya rarraba Buhunhunan hatsi 139 da Gwamnatin Tarayya ta bai wa Kano.
Ya lissafa tallafin da Gwamnatin Tarayya ta bayar wadanda suka hada da: Buhunhun shinkafa 6,000 (50kg), 42,600 buhunan, masara 17, 400 dawa da Gero 17, 400. gami da 2000 jarkar mai mai lita 20.
Ya ce Kwamitin yana neman wasu gidaje 50, 000 a cikin kashi na biyu don rarraba tallafin, baya ga gidaje 50,000 a kashi na farko yayin da ya bayyana matakin farko a matsayin babbar nasara.
Ya ce kwamitin ya sa ido sosai wajen rarraba kayayyakin, domin a tabbatar da cewa wadanda sukaci gajiyar na farko baza su samu damar amfana ba har sau biyu.
Yahuza Bello ya yi nuni da cewa Gwamnatin jihar ta kuma ba kwamitin umarnin sanya ido kan yadda ake rarraba shirin ciyar war Ramadana, ya yin da yayi alkawarin tabbatar da gaskiya da adalci a ya yin aikin.
Kwamitin ya kuma kara da cewa, baya ga gidaje 300,000 da aka yi niyya, Kwamitin kuma yana kara inganta ayyukan jinkai, gidaje da kuma gidajen marayu
No comments:
Post a Comment