Mutanen da Yan Ta’adda suka kashe a Sokoto sun karu zuwa 74, inda aka kashe Mutane 25 a kauyen Garki da kuma karin wasu Mutane 13 da aka Yanka a kauyen Dan Aduwa, 25 a Kuzari, 7 a garin Katuma sai kuma 4 wani kauyen mai suna Masawa.
A lissafin farko, an lissafa mutune 60 da Yan bindiga Dadi suka kashe a mafi munin harin da suka kai a wasu kauyuka a jihar sokoto.
Kamar yadda rahotanni daga jihar Sokoto suka bayyana, an kashe mutune kusan 60 a cikin wasu sabbin hare-haren da 'yan bindiga suka kai a ranar Laraba, 27 ga watan Mayun 2020 a wasu kauyuka na karamar hukumar Sabon-Birnin-Gobir.
Ganau ba jiyau ba, sun ce maharan sun dauki tsawon sa'o'i suna ruwan wuta a kauyukan ba tare da wani ya tunkaresu ba.
Haka zalika, wata mata da 'yan bindiga uku sun mutu a cikin wani harin da suka kai karamar hukumar Gwadabawa ta jihar.
Wani jami'in da ya samu zuwa inda al'amarin ya faru, ya sanar da BBC cewa, da misalin karfe uku zuwa biyar na yammacin Laraba ne suka samu labarin cewa Yan bindiga sun taho da babura kusan 100 daga daji.
Yan bindigar sun taho ne daga dajin dake kusa da Issa sannan sun nufi kauyukan.
A cewarsa, "Koda muka samu labari, mun je mun sanar da jami'an tsaro abinda ke faruwa.
Daga nan sai mutanen suka isa garin Garki zuwa garin Dan Adu'a."
Jami'in ya kara da cewa, "A garin Dan adu'a ne muka samu gawawwaki 13 kwance banda wadanda aka nema aka rasa a garin.
"A garin Garki kuwa abin da idanuna suka nuna mini har na dauki hoto, na ga gawawwaki 19 cif."
Ya kara da cewa, "A garin Kuzari, an kashe mutum 20 har da limamin garin A garin Kafi kuwa an kashe mutum 6, garin Masawa an harbi mutum 2."
Ya tabbatar da cewa jimillar gawawwakin da ya gani sun kai mutune 60 banda wadanda ake nema ba a gansu ba.
Ya ce, "Barayin shanu da mutane ne suka kai wadannan harin.
Mai girma gwamnan jihar kuwa ya kai jaje Sabon Birni a makon da ya wuce domin jajanta wa mutanen garin bisa ga kashe mutum 19 da aka yi."
Ya kara da cewa, "Batun jami'an tsaro kuwa, mun shaida musu abinda ke faruwa kuma sun je garin Garki amma basu da kayan aikin da za su fafata da wadannan 'yan bindigar.
"Baya ga rashin isassun kayan aiki, su kansu jami'an tsaron ba su da yawan da za su tunkari 'yan bindiga 100 da suka kawo harin."

No comments:
Post a Comment