Rashin kyakkyawan tsari ne ya haifar da mawuyacin halin da makarantun allo ke ciki - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Thursday, May 28, 2020

Rashin kyakkyawan tsari ne ya haifar da mawuyacin halin da makarantun allo ke ciki

Rashin kyakkyawan tsari ne ya haifar da mawuyacin halin da makarantun allo ke ciki ~ Sanata Shekarau..

A zantawarsa da manemna labarai tsohon gwamnan Kano Sanata Malam Ibrahim Shekarau sardaunan kano ya bayyana cewa rashin yin kyakkyawan tsari ne ya haifar da halin da makarantun allo suke ciki.

Sanata Malam Ibrahim Shekarau, ya ce ya ji wani Gwamna daga Arewacin Nijeriya na cewa wai makarantun allon nan basu tsinana wa kowa komai ba.

Shekarau, ya ci gaba da bayar da amsa da cewa :- Ba dan wadannan makarantun allon da akayi tsawon shekaru daruruwa ba, da shi wannan Gwamnan na Arewa dake kumfar baki akan makarantun allo bai iya karanta fatiha ba.

Tsari ne na shekaru da yawa daruruwa da aka yi saboda haka bazai yiwu ba wani ko wasu su zo lokaci daya su ce za su rusa wannan tsarin ba, sai dai a hankali kuma sai an yi wa tsarin wani ingantaccen tsari na musamman tukuna.

Ya ce ” a lokacin da nake Gwamnan Kano hakika na fahimci abubuwa da yawa game da tsarin makarantun allo kuma na yi tsare-tsare da dama domin inganta tsarin na kuma samu nasara kwarai da gaske.

No comments:

Post a Comment