Mataimakin Gwamnan Kebbi ya raba buhuna 400 na kayan abinci
Mai girma mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Kanal Sama'ila Yombe Dabai (mai ritaya) mni, fss, psc + (TAMBARIN ZURU) ya rarraba kusan buhuna 400 na kayan abinci a yankin jihar Kebbi ta Kudu.
Kayan abinci daya raba sun hada da; Shinkafa, Dawa da Gero.
An yi rabon ne daki-daki tun daga farkon watan Ramadan har zuwa yanzu.
Wadan da suka amfana da tallafin sun hada da; Shugabannin gargajiya, Jam'iyyar APC, Dattawa, masu ruwa da tsaki da kuma kungiyoyin siyasa.
Ita ma uwar gidan mataimakin Gwamnan Hajiya Halima Yombe ta yi nata rabon ga kungiyoyin mata a Zuru.
Mataimakin gwamnan ya nemi al'umma da su yi amfani da damar su a wannan wata mai albarka su ci gaba da addu'ar Allah ya kawo karshen wannan annoba tare da kasancewa cikin tsafta da bin shawarwarin ma'aikatan lafiya domin dakile yaduwar wannna cuta.
Har wayau, Sama'ila Yombe Dabai ya yi kira ga al'ummar jihar Kebbi da su sanya jihar da kasa baki daya cikin adu'o'in su a wannan wata.
No comments:
Post a Comment