Al’ummar Karamar Hukumar Faskari na zanga-zanga saboda yadda yankin ya koma tamkar babu tsaro sakamakon yawaitar hare-haren ’yan bindiga.
Kwana daya da kai hari a garin Kadisau, sai ga shi a safiyar Alhamis mahara sun sake kai wani harin a garin na Faskari.
Hakan yasa mutanen garin dama makwabtansu daga yankin ‘Yankara gudananar da zanga-zangar.
Kwana hudu ke nan da yin irin wannan zanga-zangar a garin ‘Yan tumaki ta karamar hukumar Danmusa.
Haka shima Kwamrad Aminu Ibrahiim Sheme ya jagoranci zanga-zangar lumana a garin Sheme karamar hukumar Faskari domin nuna fushinsu a kan yadda yan ta'adda ke kashe al'ummar karamar hukumar ba ji ba gani
Jaridar katsina daily post news ta rawaito cewa ana tsegumin rashin zuwan gwamna Masari, da sauran Yan majalissun yankin, zuwa jaje a Kadisau Faskari bisa kashe sama da mutune 60 da yan bindiga suka yi ranar Talata
Jaridar ta kara da cewa har kawo lokacin hada rahotan ba ta sami labarin zuwan wani dan majalisa tun daga Sanatan shiyyar Funtua da dan majalissar wakilan tarayya dake wakiltar mazabar Kankara, Faskari da Sabuwa ko dan majalissar jiha da yaje garin domin gane ma idonsa da kuma jajanta masu ba.
A ranar Talata ne mahara suka shiga garin Kadisau da wasu kauyuka a cikin karamar hukumar Faskari, inda suka kashe kusan mutune 65, inda akayi jana'izar mutane 53 a ranar Laraba,
yau Alhamis kuma rahoto ya bayyana cewa an tsinto gawarwaki 12 a cikin gonaki da suma yan bindigar suka kashe a ranar.
Sai dai rundunar yan sandan jihar Katsina ta ce mutune 20 ne yan bindigar suka kashe a garin.
No comments:
Post a Comment