An sauya wa dogarai 20 na Buhari wurin aiki bayan harbe-harben da yafaru a fadar Shugaban kasa - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Saturday, June 20, 2020

An sauya wa dogarai 20 na Buhari wurin aiki bayan harbe-harben da yafaru a fadar Shugaban kasa

 An sauya wa dogarai 20 na Buhari wurin aiki bayan harbe-harben da yafaru a fadar Shugaban kasa

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin sauya wa dogaransa 20 wurin aiki sakamakon harbin da akayi a fadar shugaban kasar dake Abuja.

An janye jami'an hukumar tsaron fararen kaya da jam'ian tsaro na sirri daga fadar shugaban kasar sakamakon kasa shawo kan al'amarin da sukayi, wanda ya kai ga harbi a fadar.

Ana tsammanin za a maye gurbinsu da sabbi babu dadewa.

Harbin ya kawo firgici don an yi tsammanin shugaban kasar na cikin hatsari, amma daga bisani Buhari ya bada umarnin bincike a kan al'amarin.

An yi harbin a fadar shugaban kasa bayan uwargidansa tare da 'ya'yansa uku - Zahra, Halima da Yusuf - tare da wasu jami'an tsaronsu da suka samu jagorancin ADC Usman Shugaba suka isa gidan Tunde.

Sabiu Yusuf wanda aka fi sani da Tunde, na zama a gida mai lamba 8 dake Pilot Gate a fadar shugaban kasar, Wanda ba komawa ya dawo daga Jihar legas ba dadewa Kuna Bai killace Kansas, kamar yadda aka bada umarni.

An tsare dogaran uwargidan a ranar Juma'a amma an sakesu a ranar Litinin.

Wata majiya ta sanar da The Punch cewa an sallami dogaran a ranar Laraba bayan shugaba Buhari ya duba bayanin lamarin, tare da duba karan tsayen tsaro da aka samu a jihar Kebbi a ranar 13 ga watan Maris na 2020.

Jami'in ya ce, "A kalla dogarai 20 aka mayar wajen fadar shugaban kasar sakamakon abinda ya faru a fadar da kuma na baya.

"Wannan ya hada da abinda ya faru a jihar Kebbi yayin da wani yayi yunkurin cukuikuiyar shugaban kasar yayin da yake daukar hoto da gwamnan jihar Kebbi tare da wasu jiga-jigai."

Buhari ya ziyarci Kebbi don bude gasar kamun kifi ta Argungun, yayin da wani mutum mai suna Mohammed Gundarre ya yi hanzarin kai wa shugaban kasar damka.

Daga bisani, Gudarre ya yi bayanin cewa ya so yin hannu da shugaban kasar tare da tabbatar da cewa bai so cutar da shugaban kasar ba kuma bai yi tsammanin hakan zai kawo kalubale ba.

No comments:

Post a Comment