Anyi jana'izar Mutune 52 da Yan bindiga suka halaka a Katsina, ya yinda aka kai wasu Asibiti jina-jina domin Basu kulawar gaggawa
An sake kai wa mutanen karamar hukumar Faskari hari a jiya Talata inda ayanzu anyi jana'izar mutane 52 da ‘Yan bindigan suka kashe, ya yinda aka kai wasu asibiti jina-jina domin Basu kulawar gaggawa.
Mazauna garin sunce Jami’an tsaro basu kawo agaji ba, sai bayan da yan bindigar suka Gama cin Karen su Babu babbaka, natsawon sa'a daya.
Akalla mutum 52 aka yiwa Jana iza, baya ga wasu da- Dama da aka kaisu asibiti jina-jina domin Basu kulawar gaggawa bayan sabon harin da aka kai garin Kadisau dake cikin karamar hukumar Faskari, jihar Katsina.
Mun sami labari cewa ‘yan bindigar wadanda suke dauke da manyan makamai sun shiga cikin wannan gari na Kadisau ne da kimanin karfe 4:30 na ranar Talata.
Channels TV ta ce wadannan miyagun mutane sun far ma garin ne a kan babura fiye da 100.
An kai wannan hari ne jim kadan bayan mutanen garin ‘Yan tumaki dake cikin karamar hukumar Dan musa sun fito sun yi zanga-zanga a dalilin matsalar rashin tsaron da suke fama dashi.
Mutanen yankin ‘Yantumaki sun fito kan tituna suna nuna takaicin su, bayan sace wani ma'aikacin lafiya magidanci da ‘diyarsa a cikin farkon makon nan.
Yan bindiga sun matsawa mutanen yankin karamar hukumar Faskari da Sabuwa inda a ‘yan kwanakin nan sun hallaka mutane da-dama a Kauyen Mairuwa.
Rahotanni sun bayyana cewa miyagun sun duro garin ne da sakaliyar la’asar, sun yi abin da za suyi kafin jami’an tsaro su iya kawo wani dauki bayan rana ta fadi.
‘Yan bindigar sun shafe fiye da sa’a guda suna ta’adi, sai kusan karfe 6:00 na yamma suka fita daga garin.
Sai dai ka kakin ‘yan sanda na jihar Katsina, SP Gambo Isah ya ce mutane 20 Yan bindigar suka kashe da jikkata wasu da dama, Kuma ya ce Yan bindigar sun Kai dari biyu
No comments:
Post a Comment