Haka kuma ya tabbatar da cewar za'a kara fadada ayyukan leken asiri ta hanyoyi da dama ciki harda amfani da jiragen sama karkashin wani dabarar yaki da aka kira da 'Operation Accord'
Shugaban rundinar 'yan sandan Nigeria IGP Muhammad Abubakar Adamu da shugaban 'yan sandan farin kaya DSS Magaji Bichi, da shugaban hukumar leken asirin tsaro na Nigeria Amb. Ahmed Rufai Abubakar, da Mai bawa shawara wa shugaban Kasa a kan tsaro Babagana Monguno sunyi dirar Mikiya a jihar Katsina da Jihar Sokoto
Yanzu haka manyan jami'an sun shiga ganawar sirri da Maigirma gwamnan jihar Katsina Aminu Masari tare da manyan mukarrabansa inda zasu tattauna akan yanayin tsaron jihar ta Katsina.
Shugaban rundinar 'yan sanda IGP Muhammad Abubakar Adamu ya dira a Katsina cikin shigar kalan kayan 'yan sandan kwantar da tarzoma
Haka Kuma Gwamnan Jihar Sokoto Rt. Hon Aminu Waziri Tambuwal ya karbi Bakuncin Manyan masu Kula da Shaanin Tsaro a Nigeria wadanda suka zo Sokoto bisa jagorancin Mai bawa shugaban kasa shawara Kan tsaro Gen. Mongono
Ayarin wanda Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara akan shaanin tsaro Gen. Mongono
da Shugaban Yan sanda da Director DSS da DG NIA
No comments:
Post a Comment