Gwamnan Borno ya dakatar da dukkan ma'aikatan babban asibitin Ngala dake Borno
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Baba gana Umara Zulum ya dakatar da dukkan ma’aikatan da gwamnati ke biya na babban asibitin garin Ngala dake jihar Borno.
Ma’aikatan sun hada da likitoci, malaman jinya, masu hada magani da masu gwaji na asibitin.
Wannan dakatarwar ya biyo bayan ziyarar ba-zata da yakai asibitin da karfe 11 na safiyar ranar Litinin.
Duk da karbar albashin da suke yi, ya tarar da cewa ma’aikatan sun bar asibitin a hannun wata kungiyar taimakon kai da kai wacce ke kula da majinyatan, wadanda ‘yan gudun hijira suka fi yawa a ciki.
Ngala ita ce hedkwatar karamar hukumar Ngala ta jihar Borno. Garin na yankin iyakar Borno da jamhuriyar Kamaru, Chadi, Sudan da Afrika ta tsakiya.
Bayan kwato garin da akayi daga hannun mayakan ta’addancin Boko Haram a 2015, Ngala ta kasance masaukin dubban ‘yan gudun hijira. Sun samu mafaka ne a kauyuka da gonaki sakamakon harin ‘yan ta’addan.
Kamar yadda Zulum ya saba, ya kai ziyarar ba-zata don gano halin da ma’aikatar lafiya ke ciki a jihar.
Gwamnan ya nuna matukar damuwarsa ta yadda ya tarar da cewa ma’aikatan gwamnatin basu iso ba har karfe 11 na safe.
A takaice, shugaban kungiyar dake kula da asibitin ne ya karbi Zulum bayan isarsa.
A fusace Zulum yace, “Wannan asibitin gwamnatin jihar Borno ne amma ban tarar dako ma’aikaci daya na jihar ba duk da muna biyansu albashi a kan lokaci.
“Kungiyar fi360 ce take kula da asibitin wadanda ya kamata su taimaka wa ma’aikatan. Ina umartar hukumar kula da asibitoci da ta datse biyan ma’aikatan asibitin.
Zan dawo don ganin yadda ayyuka ke tafiya daga baya. Ina fatan ganin akasin hakan.”
No comments:
Post a Comment