Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, wanda yanzu shine shugaban kwamitin kula da sojin kasar nan, Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewa 'yan majalisar tarayya da masu manyan mukamai a kasar nan ne ke morar albashi mai tarin yawa.
Sai dai kuma ya ce talakawan Najeriya ne ke cikin wani hali, jaridar Punch ta ruwaito.
Ya ce mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Ml Muhammadu Sanusi sun yi gaskiya a kan yadda ake tafiyar da gwamnatin Najeriya cike da tsada wanda yace ba dole bane hakan ya ci gaba.
Ndume ya sanar da hakan ne yayin martani ga Osinbajo da Sanusi yayin tattaunawa a kan daidatuwar tattalin arziki bayan annobar korona.
A yayin da aka tattauna da Sanusi, ya bayyana cewa tsarin da ake bi na tafiyar da gwamnati a Najeriya na nuna cewa za ta durkushe kuma ya tambayi mataimakin shugaban kasa a kan abinda gwamnatin nan ke yi don shawo kalubalen.
A martanin Osinbajo, ya ce "Ba sai an tambaya ba, an san muna ma'amala da gwamnati mai girma kuma a tsadance. Amma kuma kamar yadda kuka sani, wadanda za su saka kuri'a kan rage tsadar gwamnatin sune 'yan majalisar."
Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, wanda yanzu shine shugaban kwamitin kula da sojin kasar nan, Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewa 'yan majalisar tarayya da masu manyan mukamai a kasar nan ne ke morar albashi mai tarin yawa.
Sai dai kuma ya ce talakawan Najeriya ke cikin wani hali, jaridar Punch ta ruwaito.
Ya ce mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Muhammadu Sanusi sun yi gaskiya a kan yadda ake tafiyar da gwamnatin Najeriya cike da tsada wanda yace ba dole bane hakan ya ci gaba.
Ndume ya sanar da hakan ne yayin martani ga Osinbajo da Sanusi yayin tattaunawa a kan daidatuwar tattalin arziki bayan annobar korona.
A yayin da aka tattauna da Sanusi, ya bayyana cewa tsarin da ake bi na tafiyar da gwamnati a Najeriya na nuna cewa za ta durkushe kuma ya tambayi mataimakin shugaban kasa a kan abinda gwamnatin nan ke yi don shawo kalubalen.
A martanin Osinbajo, ya ce "Ba sai an tambaya ba, an san muna ma'amala da gwamnati mai girma kuma a tsadance.
Amma kuma kamar yadda kuka sani, wadanda za su saka kuri'a kan rage tsadar gwamnatin sune 'yan majalisar."
Ndume ya ce, "Kasafin kudinmu na tiriliyan 10 na nuna cewa kashi 30 daga ciki ne za a mika ga manyan ayyuka, kashi 70 zai tafi ne ga kanana.
No comments:
Post a Comment