Cikakken raddin da Magu ya maida wa Malami kan zargin yin sata-ta-saci-sata
PREMIUM TIMES ta tattaro Cikakken raddin martanin da Dakataccen Shugaban Rikon EFCC, Ibrahim Magu ya maida wa Ministan Shari’a, Abubakar Malami, wanda ya yi zargin cewa shi Magu na satar kudade da kadarorin da ya Æ™wato daga É“arayin gwamnati.Magu ya ce shi ba barawo ba ne, kuma bai taba satar ko sisin kwabon kowa ba.
Cikin wasikar da ya aika wa Shugaban Kwamitin da Shugaban Kasa ya kafa domin bincikensa, Magu, ya bayyana cewa Malami na jin haushin sa ne saboda ya yi ta kokarin yi wa aikin EFCC katsalandan, karan-tsaye da kuma uwa-makarbiya a kan wasu kadarori ko kudade da aka kwato.
Ya kuma ce Malami ya sha gurgunta kokarin EFCC na dawo da wasu riƙaƙƙun masu laifin satar kudade ko zamba, domin a hukunta su.
1. Na ji daÉ—i da farin ciki da har Shugaban Kwamiti ka ba ni damar kare kai na. Dama haka ka’idar adalci a bisa tsarin gudanar da tuhuma ya tanadar.
2. Wannan amsa ko raddi ko kare kai na da zan yi, kamata yayi a ce na takaita shi.
3.1 A karkashin iko na ban taba sayarwa ko bari a sayar da wasu kadarorin da aka kwato ba. Ban kuma taba karkatar da wata kadara ko wasu kudade ba.
3.2 Batun shari’ar harkallar kwangilar P&ID dai alkalan Ingila har yabon EFCC sukayi, kuma da kundin bayanan da EFCC ta rubuta mai shafi fiye da 5,000 ne lauyoyin kasashen waje suka yi amfani wajen kama P&ID da laifi.
3.3 Ko ni ko ita EFCC din ban taÉ“a yi wa wani alkali ko jami’in kotu wata barazana ba, yayin gudanar da aikin sa.
3.4 A karkashin jagoranci na ba a ragargaji kukade ko an karkatar da su ko an yi wani abu a kudundune ba.
3.5 Ban taba karkatar da kudade ko kadarorin da aka kwato ba, ballantana har a ce na azurta kai na daga wadannan kadarori da kudade.
3.6 EFCC na da aƙidar yin amfani da rubutaccen kwafen bayanai na shaida a dukkan ayyukan da take gudanarwa, ciki har da binciken yadda aka kashe Kudaden Paris Club da duk wasu binciken.
Da Gudumar Gaskiya Ake Ruguza Tubalin Ginin Makaryaci -Magu
4. Ran ka ya daÉ—e ka san idan karairayi suka yi yawa, har aka rika maimaitawa ana nanatawa, to babu abin da zai wanke zargi ko wadannan karairayin sai makamin gaskiya kawai.
Wannan shi ne dalilin da zai sa na fito na feÉ—e bakin-biri har wutsiya.
Shi Mai Girma Ministan Shari’a da ya rika kitsa min sharri da karairayi, shi ne ma ya rika kokarin dakilewa da gurgunta duk wani kokarin nasarar da EFCC ke yi, ta hanyar yin karfa-karfa ko hana ruwa-gudu a kan wasu bincike ko kadarorin da EFCC ta kwato.
5. Sannan kuma EFCC ta rika samun tsaiko daga Ofishin Ministan Shari’a a kokarin da ya riÆ™a yi wajen gurgunta shirin dawo da wasu É“arayin gwamnati ko mazambata daga kasashen waje domin a hukunta su.
6. Ba kamar yadda aka yi min sharri cewa aikin da nake yi a EFCC ba na yi da gaske kuma ba na aiki tare da nuna kishin kasa, to ga kwafe-kwafen bayanan tulin nasarorin da na samar a EFCC nan na haÉ—o maka da su, domin kayi alkalanci ka gani.
7. Ran ka ya daÉ—e, na fahimci cewa an yi min zargi kan batutuwa shida ne. Don haka ni ma zan rarraba raddi na kan zargin zuwa gida shidan, ina bin su daya-bayan-daya ina amsawa.
3 Kokawar Malami Da Magu: Wanda ya raba fadan Mai Shari’a Da Dan Sanda bai sha Kallo Ba:
Martanin Ga Rahoton Kwamitin Shugaban Kasa Da Ya Binciki Kudade Da Kadarorin Da EFCC ta Kwato.
1. Ban yarda da sakamakon wannan rahoto da ya ce an tabka rashin gaskiya, ‘yar-burum-burum da karkatar da kadarori a EFCC ba. Rahoton kirkirarren tuggu ne kawai don a É“ata min suna kuma a zubar da kimar EFCC.
Karairayi ne kawai aka kitsa mani. Ban saci ko sisin kwabo ba, ban karkatar da ko kadara guda daya ba.
Ina ƙalubakantar shi wanda ke zargi na ya kawo shaida ko da guda daya ce da ta nuna na karkatar da kudade ko kadarorin da aka kwato a karkashin yaki da cin hanci da rashawa da zambar kudade.
Wannan rahoto algungumanci ne kawai cike fal a ciki. Domin ba a bai wa Hukumar EFCC kwafen zarge-zargen da aka yi mata ba, ballantana a kira jami’an hukumar su kai ko su bayar da bayanin inda ‘yan kwamiti ke tababa, zargi ko Ikirarin an yi ba daidai ba.
Ya zama rahoton rashin adalci, tunda dai ni da ake zargi ba a gayyace ni na kare kai na ba. Wannan kuwa a duk duniya babu inda za a gamsu da irin wannan hukunci, domin ba a ji ta bakin wanda ake zargi ba.
Ni ban taɓa maida dalolin kudaden da EFCC ta kwato zuwa naira ba a rubuce. Babu inda na kira dala da naira ko sau daya. Idan akwai kuma to a bayar matsayin shaida a kai na.
Ban san inda suka rakito adadin naira bilyan 39, 357,608, 119 43 ba, suka ce wai na maƙale kudaden ban saka su cikin adadin kudaden da nace na kwato ba.
4 An Kure Ramin Karya:
Shi kan sa magulmacin da yace bai haÉ—a wa gwamnati da wadannan bilyan 39 da doriya ba, ai ya dawo ya ce kudaden suna Asusun Ajiyar Gwamnatin Tarayya a Babban Bankin CBN.
Wannan kuwa ya karyata duk wani makaryacin da yace na karkatar da kudaden ban lissafa da su ba.
Adadin kudaden da Kwamitin Binciken Kudade da Kadarorin Gwamnati da EFCC ta kwato, ya yi azarɓaɓin zargi na da hukumar baki daya da karkatar da kudade.
Bai yi la’akari da cewa akwai hukumomi da ma’aikatun da idan an kwato kudaden su da aka sace, to kai-tsaye su ake tura wa kudaden su a cikin asusun su, ba a cikin asusun gwamnatin tarayya na bai daya da ke CBN ba.
Bai yi la’akari da cewa akwai hukumomi da ma’aikatun da idan an kwato kudaden su da aka sace, to kai-tsaye su ake tura wa kudaden su a cikin asusun su, ba a cikin asusun gwamnatin tarayya na bai daya da ke CBN ba.
Wadannan hukumomi kuwa sun hada da:
FIRS, NNPC, AMCON, Hukumar Kwastan ta Kasa, Bankunan Kasuwanci, da sauran wasu cibiyoyi da daidaikun jama’a.
Magu ya ci gaba da kan sa tare da haÉ—awa da kwafen takardun hujjoji.
Cikin wadanda ya kara yin magana dalla-dalla, har da yadda jirgin ruwan da EFCC ta kama ya nutse cikin aljihun Malami.
Akwai sauran zarge-zarge da dama wadanda Magu ya rika bi filla-filla ya na cewa karairayi da sharri Minista Abubakar Malami yayi masa
No comments:
Post a Comment