Fadar Shugaba Najeriya ta bada umarnin gudanar da bincike dangane da abin kunyar da ya faru a tsakanin jami’an tsaron Uwargidan Shugaba Buhari da wasu jami’an tsaron fadar dangane da neman tilistawa daya daga cikin masu taimakawa shugaban Kasar killace kansa na makwanni biyu, sakaamakon wata tafiya da ya yi zuwa jihar Legas, inda cutar COVID - 19 tafi Kamari.
Tun a ranar Juma’a Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta aike da sako ta kafar twitter Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta yi zargin cewar hukumar 'Yan Sandan kasar ta tsare jami’an kula da lafiyar ta sakamakon zargin harbi da bindiga a fadar shugaban kasa,inda ta bukaci Sufeto Janar na 'Yan Sanda da ya saki jami’an na ta domin kaucewa jefa rayuwar su cikin hadari.
Rahotanni sunce tsare mutanen ya biyo bayan wata matsala da aka samu tsakanin Uwargidan shugaban da wani jami’in shugaban kasa da ya koma Abuja daga Lagos yaki amincewa ya killace kan sa a matsayin kariya daga cutar coronavirus.
Kuna iya latsa alamar sauti dake katsa don sauraron abin masu sharhi ke cewa da martanin gwamnati cikin rahoton Mohammed Kabir Yusuf daga Abuja.
No comments:
Post a Comment