Ahmad Lawan ya yi magana ne da ‘yan jarida a karshen makon da ya gabata, inda ya zargi siyasar kasashen Duniya da hannu wajen kin bari a saidawa jami’an tsaro kayan yaki.
Lawan yake cewa rashin samun manyan makaman da ake bukata, ya kawowa jami’an tsaro cikas.
Da yake yi wa manema labarai bayani, sanata Dr. Ahmad Lawan ya ce ana batawa dakarun sojojin Najeriya lokaci fiye da yadda ya kamata kafin su iya fansar makaman yaki.
Shugaban majalisar yake cewa aiki ya yi wa sojojin Najeriya yawa, sannan kuma akwai bukatar a tanadi kayan yaki kafin a iya shawo kan matsalar rashin tsaron da ake fama dashi.
“Kusan ka iya cewa muna fama da matsalar siyasar Duniya.
Na san cewa wajen kokarin sayen kayan jiragen yaki, ya kan dauke mu tsawon lokacin watanni shida ko ma tara.”
Sanatan yace akwai rashin adalaci a harkar da take tafiya: “Idan wata kasar ta rubutawa gwamnati takarda cewa tana son makamai, sai a saida mata a cikin wata guda ko kuma biyu.”
“Saboda haka abubuwa ba su tafiya daidai, wannan yana cikin kalubalen mu.
Za mu cigaba da kokarin tattaunawa da wadannan kasashe da ba su gane inda mu ka dosa ba.”
“Jami’an tsaronmu kuma suna bukatar karin dakaru da kudi.”
“Muna bukatar karin jami’an ‘yan sanda, masu kula da shige da fice da kusan duk wasu bangarorin tsaro.”
Dr. Lawan yake cewa Najeriya tana kuma da bukatar ma’aikata.
“Gwamnati tana bakin kokari wajen samun kayan aiki da makamai.”
No comments:
Post a Comment