Kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar korona a Najeriya ya sanar da matakin rufe kananan hukumomi 18 cikin 774 da ke Najeriya.
A cewar kwamitin, wadan nan kananan hukumomin su ne suke da kashi 60 cikin 100 na mutum 24,077 da suka harbu da cutar korona.
Kwamitin ya bayyana haka ne ranar Litinin.
Shugaban kwamitin kuma Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya kuma ce za a bude makarantu ga daliban da ke shirin rubuta jarrabawa - 'yan aji shida a firamare da 'yan aji uku na karamar sakandare da kuma 'yan aji uku na babbar sakandare.
Hakazalika, gwamnatin tarayyar ta amince da bude shige da fice tsakanin jihohin kasar nan, amma matukar ba a zarta lokutan doka ba.
Gwamnatin tarayyar ta kara da amincewa da sauka ta tashin jiragen sama a cikin fadin kasar nan kadai.
No comments:
Post a Comment