An hana Magu gabatar da daftarin hujjoji gaban kwamitinin bincike
Shugaban hukumar EFCC da aka dakatar, Ibrahim Magu ya gurfana gaban kwamitin bincike na fadar shugaban kasa
- Kwamitin na tuhumar Magu kan kadarori da kudaden da hukumar EFCC ta kwato daga hannun barayin kasa
- Wahab Shittu, lauyan Magu, ya ce an hanasu gabatar da hujjojin kariya gaban kwamitin.
Wani rahoto da jaridar Vanguard ta wallafa ya yi nuni da cewa tsohon shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu da lauyansa Wahab Shittu a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuli sun so gabatar da wata takarda mai dauke da shafuka 34 gaban kwamitin.
Magu ya ƙalubalanci Malami ya kawo shaida guda daya tal inda ya karbi toshiyar baki
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/magu-ya-alubalanci-malami-ya-kawo.html
Takardun na dauke da hujjojin kariya ga Ibrahim Magu, sai dai rahotanni sun bayyana cewa an hanasu gabatar da hujjojin gaban kwamitin fadar shugaban kasar.
Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa Magu da lauyansa sun bayyana gaban kwamitin binciken dake karkashin mai shari'a Ayo Salami da misalin karfe 1 na rana har zuwa karfe 6 na yamma.
Rahotanni sun bayyana cewa ya isa fadar shugaban kasar tare da lauyansa Shittu da kuma wasu hadimansa.
Sai dai an ruwaito cewa Magu da Shittu ne kawai aka bari suka shiga cikin babban dakin gudanar da binciken, inda suka zauna na tsawon awanni.
Kundin hujjojin mai dauke da shafuka 34, ya kunshi hujjoji a rubuce, da hotuna, an kawo shi ne da nufin gamsar da kwamitin cewa duk tuhumar da ake yiwa Magu karya ce tsagoronta.
Jaridar Vanguard ta yi nuni da cewa lauyansa, Shittu, a wayar tarho ya ce ba a bari suka gabatar da wannan kundi ba a ranar (Alhamis).
An hana Magu gabatar da hujjoji gaban kwamitinin bincike Source: UGC "Amma dai zamu koma gobe (Juma'a)," a cewar lauyan, duk da cewa bai bayyana dalilin da yasa aka hanasu gabatar da hujjojin ba.
Kwamitin fadar shugaban kasar na tuhumar Magu akan kadarori da kudaden da hukumar EFCC ta kwato daga hannun wadanda suka saci kudin jama'a.
Magu ya fallasa Yadda Malami ya karya doka, yayi gwanjon kayan satar da EFCC ta kama
No comments:
Post a Comment