An yi jana'izar Tolulope Arotile, matukiyar jirgin saman yakin Najeriya ta farko, wacce ta mutu sanadin bangajewar da mota tayi mata a jihar Kaduna a makon jiya.
Manyan jami'an rundunar sojin sama da jami'an gwamnati ciki har da gwamnan jihar Kogi, mahaifar Ms Arotile ne suka halarci jana'izar tata da aka yi a babbar makabartar sojin Najeriya da ke Gudu a Abuja.
An bayyana marigayiyar da cewa ta bayar da gudunmuwa sosai a yaki da Æ´an bindiga masu fashin daji a jihar Neja inda ita ce ke tuka jiragen rundunar Gama Aiki.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina mata bisa sadaukarwar da ta yi wajen ci gaban kasar.
Babban hafsan sojin saman kasar Air Marshal Sadique Abubakar ya ce mutuwar jami'ar babban rashi ga rundunar tare da jajanta wa iyalanta a madadin dukkanin jami'an rundunar sojin sama na Najeriya.
Sakamakon binciken farko da runduar sojn kasar ta fitar ya nuna cewa wasu tsoffin abokan karatunta ne suka buge ta da mota ta baya lokacin da suka gan ta kwatsam a yayin da suka yi kokarin juyawa domin isa gare ta.
No comments:
Post a Comment