Kwamitin riƙo na jam'iyyar APC Ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ya zaɓi gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma da zasu jagoranci kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar All Progressives Congress (APC) gabanin zaɓen gwamna a jihar Edo.
Ganduje zai yi aiki a matsayin shugaba yayin da Uzodinma zai yi aiki a matsayin Mataimakin Shugaba, sannan Hon. Abbas Braimoh a matsayin Sakataren kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar jam’iyyar APC mai wakilai 49.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC na kasa, Yekini Nabena.
Sanarwar ta ce, shugaban kwamitin kula da tsare-tsare na kasa na jam’iyyar APC Mai Mala Buni ya ba da izinin kunɗin tsarin mulki na kamfe ɗin na ƙasa, da za'ayi a ranar 19 ga Satumbar, 2020.
Nabena ya ce za a ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen a ranar Litinin, 6 ga Yuli 2020 a sakatariyar ƙungiyar na kasa.
Membobin ƙungiyar kamfe ɗin sun haɗa da: Sen. Ovie Omo-Agege, gwamna Inuwa Yahaya, gwamna Yahaya Bello, gwamna Baba jide Sanwo-Olu, Chief ohn Odigie-Oyegun, Comrade Adams Oshiomhole, Sen. Aliyu Magatakarda Wamakko, Sen. Godswill Akpabio, Sen. Orji Uzor Kalu, Sen. Owelle Rochas Okorocha, Timipre Sylva, Dr. Pius Odubu, Sen. Degi Eremiemyo Biobaraku, Farfesa Oserheimen A. Osunbor, Emmanuel Eweta Uduaghan, Sen. John Owan Enoh, Hon. E.J. Agbonayiman, Engr. Babachir Lawal, Yarima B.B Apugo, Gen. Charles Airhiavbere Hon. Peter Akpatason, Hon. Patrick Aisowere da Hon. Johnson Oghuma.
Sauran membobin sune Hon. Farfesa Julius Ihonvbere, Hon. Pally Iriase, Hon. Dennis Idahosa, Misis Rachel Akpabio, Mr. Bolaji Afeez, Engr. Gabriel Iduseri, Chief Cairo Ojougboh, Patrick Obahiagbor, Chief Ayiri Emami, Hon. Abubakar Adagu Suberu, Usman Nahuche, Engr. Chidi Orji, Dr. Almajiri Geidam, Sen. Sa’idu Umar Kumo, Chief Pius Akinyelure, Engr. Chris Ogiemwonyi, Cif Solomon Edebiri, Farfesa Ebegue Amadasun, Hon. Asabar Uwulekue, Hon. Osaro Obaze, Cif Samuel Ogbuku, Miss. Rinsola Abiola, Theresa Tekenel da Hon. Abbas Braimoh.
No comments:
Post a Comment