Mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai, Femi Adesina shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata
Sanarwar martini ne ga kiran da Majalisar Dattawa tayi ga shugaban kan ya kori manyan hafsoshin tsaron.
Adesina, a cikin martanin mai taken “Manyan hafsoshin tsaro: Matsayin fadar shugaban kasa shawarar Majalisar Dattawa”, ya ce shugaban zai yi duk abin da ya san zai haifar wa kasar da mai ido.
“Fadar Shugaban Kasa ta saurari sakon Majalisar kuma tana kara jaddada musu cewa ikon nadawa ko sauke manyan hafsoshin tsaro alhaki ne da ya rataya a wuyan Shugaban Kasa.
“A matsayinsa na Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, zai yi duk abin da ya san zai haifar wa da kasar da mai ido a kowane lokaci”, inji sanarwar.
A ranar Talatar Majalisar Dattawa ta bukaci manyan hafsoshin tsaron kasar da su sauka daga mukamansu saboda abin da Majalisar ta kira gazawarsu a bangaren tsaro bayan da Sanata Ali Ndume (Borno, APC) ya gabatar bukatar hakan a gaban majalisar.
Majalisa ta bukaci Buratai da sauran shugabannin tsaro su yi murabus
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/majalisar-dattawa-ta-buaci-shugabannin.html
Majalisa ta bukaci Buratai da sauran shugabannin tsaro su yi murabus
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/majalisar-dattawa-ta-buaci-shugabannin.html
No comments:
Post a Comment