Jerin Abubuwa 14 da ya kamata ka sani kafin cike aikin ɗan sanda - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Saturday, July 11, 2020

Jerin Abubuwa 14 da ya kamata ka sani kafin cike aikin ɗan sanda

Jerin Abubuwa 14 da ya kamata ka sani kafin cike aikin ɗan sanda

Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana shirin ɗaukan sabbin jami'an 'an sanda 'kurata' kuma ta yi bayanin yadda masu sha'awa zasu iya nema da sharudan da za'a cika.

Kakakin hukumar, DCP Frank Uba, ya bayyana haka a jawabin da ya saki ranar Asabar, 11 ga Yuli, 2020.

Za'a fara rijistan daga ranar 14 ga Yuli zuwa 23 ga Agusta, 2020 kuma za'ayi rijista a adireshin yanar gizo 'www.policerecruitment.gov.ng'

Ga jerin sharrudan da aka gindaya ga masu nema:

1. Wajibi ne ka kasance haifaffen dan Najeriya kuma kana da lambar katin zama dan kasa

2. Wajibi ne ka kasance mai Credit akalla 5 a jarrabawar WAEC, NECO, GCE da NABTEB tare da Turanci da Lissafi

3. Kada kayi kasa da shekaru 17 da haihuwa kuma kada kafi shekaru 25

4. Kada tsayinka ya yi kasa da 1.67cm ga maza kuma 1.64cm ga mata

5. Kada fadin kirjinka yayi kasa da inchi 34

6. Ban da mata masu juna biyu

7. Kada ka kasance mai kashi a gindi da rashawa

8. Kada ka kasance mai nakasa a harshe, kurma ko bebe

9. Kada ka kasance mai gaucaccen haba

10. Kada ka kasance mai budadden kafa

11. Kada ka kasance mai lankwashasshen kafa

12. Kada ka kasance mai nakasa a hannu

13. Kada ka kasance mai ciwon ido, ko mai ido daya

14. Kada ya kasance an taba yanke maka wani sashen jiki


No comments:

Post a Comment