Dakarun Operation Lafiya Dole sun halaka mayakan Boko Haram 75 tare da ƙwato miyagun makamai daga wurinsu a yankin arewa maso gabas.
- Mayaƙan na Boko Haram sun tarar da ajalinsu ne yayin arangama 17 da suka yi da dakarun sojin daga ranar 1 ga watan Yuni zuwa 30 ga watan Yuni.
- An kuma kama matan kwamandan Boko Haram da ke Gajingi a karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa su biyu, Aishatu Manye da Kelune Mate
Najeriya ta sami sabon jirgin yaƙi na leƙen asiri
Rundunar Operation Lafiya Dole ta kashe mayaƙan Boko Haram 75 tare da samo miyagun makamai daga wurinsu a yankin arewa maso gabas.
Shugaban fannin yaɗa labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche ne, ya tabbatar da aukuwar hakan ta wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi.
Kamar yadda yace, an kashe mayaƙan ne sakamakon harin da dakarun sojin suka kai wanda yasa mayaƙan suka mutu tare da samo wasu makamansu.
Enenche ya ce mayakan Boko Haram din su tarar da ajalinsu ne yayin arangama 17 da suka yi da dakarun sojin daga ranar 1 ga watan Yuni zuwa 30 ga watan Yuni.
Sojin sama sun ragar-gaza sabbin shugabannin boko haram
Ana samun manyan nasarori na murkushe mayaƙan ta'addancin da suka addabi yankin arewa maso gabas.
An samu halaka wasu, an samu makamai yayin da wasu daga ciki suka miƙa wuya ga dakarun sojin.
"A ƘoƘarin da dakarun sojin ke yi na kawo ƙarshen Boko Haram, dakarun rundunar Operation Lafiya Dole sun kai hari 17 ga mayaƙan, tare da kashe 75 daga ciki,"
Daga cikin makaman da aka samo akwai bindigar ɓaro jiragen sama 1, bindiga kirar AK 47 13, bindigar toka 21 da sauransu.
Akwai bama-baman masu linazami, harsasai 1018 da kuma tutocin Boko Haram 2.
Ina cikin barci mata ta yanke min Azzakari
Mai magana da yawun rundunar ya yi bayanin cewa an samu motar yaki daya, motar dasa bam daya, mota kirar Toyota Starlet daya da sauransu, Channels TV ta ruwaito.
Ya yi jajen yadda daya daga cikin dakarun su ya rasa ransa yayin da wasu suka samu raunika.
An ceto mutum 35, daga ciki 18 mata ne sai ƙananan yara 16 da magidanci daya.
Ganduje ya wai wayi yaran kano da aka sace, ya ɗauki ƙwaƙw ƙwaran mataki
A yayin karin bayani, Enenche ya ce hudu daga cikin 'yan ta'addan da suka kama akwai mata biyu, Aishatu Manye da Kelune Mate.
An gano cewa matan kwamandan Boko Haram ne da ke Gajingi a karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa.
No comments:
Post a Comment