Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta kama gaggan 'yan fashi da makami 10 da masu garkuwa da mutane 33 a yankuna daban-daban na jihar.
Haka zalika rundunar 'yan sandan ta samu nasarar cafke wasu mutum 16 masu tayar da zaune tsaye da ake zargi da haddasa rikicin kabilu kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
Olugbenga Adeyanju, kwamishinan 'yan sanda na jihar, shi ne ya sanar da haka a taron manema labarai da aka yi ranar Litinin a garin Yola, babban birnin jihar.
Mista Adeyanju ya ce, an kama ababen zargin ne daga ranar 1 ga Yuli, kawo yanzu, sakamakon kokarin da jami'an 'yan sanda ke ci gaba da yi.
Akpabio ya yi fallasa, ya bayyana wadanda aka bai wa kwangila
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/akpabio-ya-fallasa-waanda-aka-bai-wa.html
Ya ce: "Rundunar 'yan sandan ta cafke masu garkuwa da mutane 33, 'yan kungiyar asiri 2, 'yan fashi da makami 10 da kuma mutum 16 masu haddasa husuma ta kabilanci a jihar."
"An samu nasarorin ne sakamakon fafutikar da jami'an tsaro suka yi wajen kwantar da tarzoma tare da samun goyon baya daga kwararrun mafarauta, gwamnati da mutanen jihar."
Mun kama muggan makamai da suka hada da manyan bindigogi guda ciki har da kirar AK47 guda 5.
"Sauran makaman sun hada da alburusai 328, sassan jikin dan Adam, mota kirar Toyota mai ɗauke da lambar RBH 186 AA, babur mai kafa uku da kuma tsabar kudi har naira 58,420."
Kwamishinan ya ce waɗanda ake zargi sun shiga hannu ne a wasu kananan hukumomin jihar da suka hada Fufore, Maiha, Gombi, Mubi ta Arewa da Yola ta Arewa.
Ya ce mutane 16 da aka kama bisa zargin haddasa rikicin kabilanci an kama su da muggan makamai, sannan suna da hannu a rikicin baya-bayan nan tsakanin kabilun Lunguda da Waja a karamar hukumar Guyuk da Lamurde.
Shugaban hukumar NDDC ya Suma ya yin amsa tambayoyi
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/shugaban-hukumar-nddc-ya-suma-ya-yin.html
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/shugaban-hukumar-nddc-ya-suma-ya-yin.html
No comments:
Post a Comment