Yara kusan miliyan 10 za su daina karatu har abada
Kungiyar Agaji ta Save the Children ta ce, annobar coronavirus ta haifar da dari-dari a bangaren ilimi, inda kananan yara kusan miliyan 10 ke fuskatar barazanar ban-kwana da makaranta har abada.
Save the Children ta Birtaniya ta bada misali da alkaluman da Hukumar Raya Ilimi, Kimiya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta fitar da ke nuna cewa, a cikin watan Afrilu, matasa biliyan 1.6 ne suka gaza zuwa makarantu da suka hada da jami’o’i saboda matakan da aka dauka na yaki da cutar COVID-19.
Wannan adadi na biliyan 1.6 na a matsayin kashi 90 cikin 100 na daukacin daliban da ake da su a duniya, yayin da Save the Children ta ce, a karon farko a tarihin bil’adama, an katse wa daukacin yara karatunsu a fadin duniya.
A cikin rahoton da ta fitar, Kungiyar Agajin ta ce, mummunan tasirin da coronavirus ya yi kan tattalin arziki, zai tilasta wa karin yara miliyan 90 zuwa miliyan 117 tsunduma cikin talaluci, lamarin da zai shafi karatunsu kai tsaye.
Kungiyar ta kara da cewa, al’adar nan ta tilasta wa kananan shiga aikin kwadago ko kuma yi musu auren wuri don taimaka wa iyalansu, za ta sanya yara kimanin miliyan 9.7 yin ban-kwana da karatu har abada.
Save the Children ta ce, dole ne gwamnatoci su gaggauta zuba karin jari a fanin ilimi a daidai wannan lokaci da yaran ke fuskantar barazanar.
No comments:
Post a Comment