MAKOMA A SIYASAR KANO: KAFIN DAMA TA KUBUCE.. - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Sunday, February 3, 2019

MAKOMA A SIYASAR KANO: KAFIN DAMA TA KUBUCE..

MAKOMA A SIYASAR KANO: KAFIN DAMA TA KUBUCE...
Mutane da yawa da ya kamata su yi magana a kan siyasa suna kin yi don gudun cin mutunci daga jahilai da wawayen gari (sufaha'u), amma wannan ba uzuri ba ne a gaban Allah. Masu gudun cin mutunci idan ba su yi magana ba abinda ya fi mutunci za'a ci musu: addininsu da rayukansu da goben 'ya'yayensu. Siyasa ta fi karfin a kyale ta a hannun 'yan tsirarun masu mulki da 'yan rakiyarsu wadanda yawanci ba su san inda kansu yake musu ciwo ba.

Ya kamata malamai da masana da 'yan Boko masu kishin al'umma su fito su yi magana domin fuskantar da jama'a ina ya kamata su jefa kuri'unsu. Na fuskanci wasu sun yi haka dangane da zaben 'yan takarar shugaban kasa kuma sun kyauta, sun yi nasiha ga al'ummarsu, sun sauke nauyin da yake kansu. Kuma zagin sufaha'u bai rage musu kome ba, sai ma karin lada in Allah ya yarda.

Irin abinda wadancan suka yi na fitowa karara su nuna wanda ya fi cancanta a zaba a matsayin shugaban kasa shi nake ganin ya kamata shuwagabannin al'umma a jihar Kano su fito su yi dangane da zaben gwamna. Kuma suna iya yin hakan a dunkule, a hade, ko kuma a matsayin daideku.

Muna da shugabanni, masana, masu hikima da gogewa, wadanda suka san siyasarmu ta Kano, kuma suka san dukkanin manyan 'yan takarar mukamin gwamna a jihar, amma sun koma gefe, sun yi gum! A ganina wannan bai dace ba, domin yana iya kaiwa ga cin amana irin wanda Allah yake kama masana a kansa, sawa'un malaman addini ne ko masu ilmin zamani.

Ina sane da yadda tarbiyya ta lalace a Kano da ma sauran jihohin Arewa da Nijeriya baki daya, inda yara da gama-garin mutane suke haikewa shugabanni da zarar sun furta abinda ya saba son zukatansu. Kuma hakan ya sanya da yawa daga cikin ma'abota ra'ayi da gogewa sun ja da baya, suka bar fagen ga jahilai da 'yan baka, wadanda hakkinsu shi ne su saurara idan masana sun yi magana domin su koya, amma ba su bude baki suna magana a kan makomar al'umma da hujjar cewa wai su ma suna da 'yancin fadin albarkacin baki ba.

Wannan takaitacciyar makala nasiha ce da karfafa guiwa ga shugabanninmu cewa kada tsoron zagi da cin mutunci ya sa su gaza a wajen aikinsu na jagoranci. Yaushe mai yin abu don Allah zai damu da zagi? Kuma shin ba'a zagi annabawa ba? Akwai annabin da ya bar isar da manzanci da fadin gaskiya don zagin masu zagi?

Har abada a cikin al'umma ba za'a rasa wawaye da jahilai ba, kuma a hakika ma su suka fi yawa. To sai a bar musu makomar al'umma a hannunsu? Lallai shugabanni da masana su fito su fadi gaskiya, kuma su yi hakuri da jahilcin jahilai da wawancin wawaye.

A fito a yi magana dangane da makoma a siyasar Kano tun DAMA ba ta KUBUCE ba.

No comments:

Post a Comment