Amurka ta damu game da taɓaɓarewar siyasar Jihar Edo
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya bayyana damuwa game da "taɓaɓarewar siyasar Jihar Edo", wadda hukumar INEC ke shirin gudanar da zaɓen gwamna a watan Satumba.
"Amurka ba ta ji daɗin abubuwan da ƴan siyasa (a Edo) ke aikatawa ba," a cewar wata sanarwa da ofishin ya wallafa a shainfsa na Twitter ranar Juma'a.
Sanarwar ta ƙara da cewa Amurka za ta tallafa wa Najeriya wurin tabbatuwar dimokuraɗiyya "matuƙar dai za a riƙa bai wa talakawan Najeriya waɗanda suka zaɓa".
Gwamnan Edo ya ƙwaye Rufin Majalisar Dokokin Edo
https://www.arewagist.com.ng/2020/08/obaseki-ya-cire-rufin-majalisar-dokokin.html
Jijiyoyin wuya sun fara tashi a Jihar Edo da ke Kudu maso Kudancin Najeriya ne bayan rantsar da mambobin majalisar dokokin jihar su 14, waɗanda suka yi yunƙurin karɓe ikon majalisar.
A watan Satumba mai zuwa ne za a gudanar da zaɓen gwamna a jihohin Edo da kuma Ondo.
Amurka ta ce tana kallon Najeriya a matsayin "uwa a Afirka" sannan ta yi kira ga masu ruwa da tsaki ciki har da hukumar zaɓe da su tabbata an yi zaɓen adalci kuma mai cike da zaman lafiya
No comments:
Post a Comment