Zulum ya kai wa ƴan gudun hijira 80,000 tallafi a Monguno - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Friday, July 31, 2020

Zulum ya kai wa ƴan gudun hijira 80,000 tallafi a Monguno

Zulum ya kai wa ƴan gudun hijira 80,000 tallafi a Monguno

Duk da harin da aka kai wa tawagarsa a garin Baga, Gwamna Babagana Umara Zulum ya cigaba da ayyukan jin ƙansa a Munguno inda ya kai wa yan sansanin gudun hijira kimanin 80,000 kayan tallafi.

Gwamnan ya isa Munguno a ranar Litinin tare da tawagarsa inda suka raba wa 'yan sansanin gudun hijira kayan tallafi a Marte, Guzamala, Kukawa, Nganzai da Monguna.

An rabar da dubban buhunan hatsi, man girki da wasu kayayyakin ga mutanen da ke sansanin yan gudun hijirar da sauran mabukata a garuruwan da sansanin suke.

An raba wa mazaje buhunnan hatsi da man gyada yayin da mata kuma kowannensu aka bata N5,000.

Kwamandan rundunar Soji da ke barikin sojoji ta Nasara a Monguna ya yabawa jajircewa irin ta Gwamna Zulum bisa ziyarar da ya kai wa sojojin.

Kafin ya bar Monguno zuwa Maiduguri, Farfesa Zulum ya duba wasu ayyuka da ake gudanarwa da suka hada da ginin Babban Makarantar Sakandare ta Islamiyya, ginin gidaje 1000 da ginin babban makarantar firamare.

Da ya ke wurin aikin ginin gidajen 1000 da Babban Makarantar Sakandare ta Islamiyya, Zulum ya bukaci 'yan kwangilar su cigaba da aiki mai kyau da suka fara.

"Na ga aikin ku a Uyo, na gani a Mbala. Ban gamsu da irin aikin da nake gani a nan ba.

Ya kumata mu janyo hankalinku game da ingancin aikin. Ba wai ginin kadai bane damuwarsu, muna son aiki mai kyau."

No comments:

Post a Comment