An buƙaci ayi bincike kan alaƙanta gwamna da Boko Haram
Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta yi kira ga jami'an tsaro da su tsananta bincike kan zarge-zargen da Dakta Obadiah Mailafiya yayi domin gano gaskiyar lamari bisa zarge-zargen da yake yi.
A wannan makon ne dai Dakta Obadiah Mailafiya yayi zargin cewa akwai wani gwamna daga arewacin Najeriya wanda shi ne kwamanda na Boko Haram.
Sai dai a wani martani shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa Simon Lalong kuma wanda shi ne gwamnan jihar Filato ya fitar, ya bayyana cewa ya zama dole ayi bincike kan wannan zargi da Dakta Mailafiya yayi.
Ya kuma buƙaci Mai lfaiya da duk wani ɗan Najeriya da ke da bayanai da za su taimaka wa jami'an tsaro wurin daƙile masu tayar da ƙayar baya da su fito su taimaka, sai dai ya ce yana fata kuma wannan zarge-zarge da Dakta Mailafiya yayi ba yana ƙoƙarin sanyaya gwiwar gwamnonin arewa ba ne daga ƙoƙarinsu na kawo ƙarshen rashin tsaro.
Ya kuma bayyana cewa ƙunigyar gwamnonin ba ta goyon bayan duk wata ƙungiyar masu aikata laifi ganin cewa su da iyalansu ba su tsira ba, inda har ya yi misali da harin da aka kai wa gwamnan Borno Babagana Umara Zulum.
Tuni dai hukumar DSS ta gayyaci Dakta
No comments:
Post a Comment