Amurka ta bayyana cewa ƙungiyar ISIS da Al-Qaeda sun soma kutsawa zuwa yankin arewa maso yammacin Najeriya.
A taron manema labarai, kwamandan dakarun Amurka na musamman a Afrika, Dagvin Anderson ya ƙara da cewa ƙungiyar Al-Qaeda kuma na kara faɗaɗa rassanta a yankunnan ƴasashen yammacin Afrika.
Bayanan wadanda aka wallafa a shafin intanet a ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Anderson y ace Amurka za ta ci gaba da haÉ—a gwiwa da Najeriya domin musayar bayanan sirri.
A cewarsa hare-haren Al-Qaeda sun janwo rufe makarantu fiye da 9,000 kuma 3,000 daga ciki a kasashen Mali da Burkina Faso.
"Muna tattaunawa da Najeriya kuma za mu ci gaba musayar bayannan sirri domin kara fahimtar ayyukan masu tsattsaurar ra'ayi," in ji Anderson.
"Hakan na da matukar mahimmanci gannin yadda kungiyar tayi É“arna a jihar Borno kuma a yanzu ta soma samun gindin zama a yankunan arewa maso yammacin Najeriya."
Anderson ya ce idan ana son taimakon kasashen waje yayi tasiri a yaƙi da ta'addanci a Najeriya dole ne gwamnatin kasar ta shiga sawun gaba wajen murkushe ƙungiyar.
"A kan batun Najeriya, kasar na da mahimmanci a yammacin Afrika. Akwai buƙatar gwamnati ta shiga gaba domin zubarar da yunƙurin yaƙi da ƙungiyar".
Mutane 135 sun mutu yayin da mutane 5,000 suka jikkata Sakamakon fashewar wasu sinadarai a Lebanon
Garambawul Kan Tsaro
A makon nan ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da umurnin ayi garambawul ga baki daya tsarin tsaro a ƙasar.
Sai dai da dama daga cikin 'yan ƙasar na saka ayar tambaya kan me shugaban ƙasar ke nufi da garambawul da kuma manufarsa a wannan karon.
Kuma abin da tambaya shi ne ko wannan garambawul zai yiwu idan hafsoshin tsaro na kan muƙamansu?
Group Captain Sadik Shehu mai sharhi kan al'amuran tsaro a Najeriya ya ce ba ya tunanin cewa ci gaba da zaman manyan hafsoshin sojin kan muƙamin su zai kawo cikas ko kuma wata matsala ga yin wannan garambawul ɗin.
A cewarsa, shugaban ƙasa ke da wuƙa da nama a hannunsa, idan yana so ayi wannan garambawul ɗin ko hafsoshin suna kan muƙaminsu hakan zai yiwu.
Ya ce "soja a dimukuraÉ—iyya, gaskiya ace mashi yaje yayi ne kawai, ko waÉ—annan mutane suna nan, ko ba sunan za a yi, su an É—auke su aiki ne.
"Idan shugaban ƙasa da ministan tsaro da ma'aikatar 'yan sanda suka ce ana so ayi wannan garambawul ɗin, a gaskiya zamansu ko rashin zamansu ba zai hana ayi wannan aikin ba.
Zulum ya ce jami'an tsaro na yin zagon ƙasa a yunƙurin kawar da ƙungiyar Boko Haram
No comments:
Post a Comment