Gwamnonin APC sun kaiwa Gwamna Zulum ziyara tare da jaje bisa harin da aka kai masa a garin Baga, karamar hukumar Kukawa, ranar Laraba, 29 ga Yuli, 2020.
Zulum ya yi bayani ga gwamonin APC
A ranar Lahadi, inda ya bayyanawa musu cewa ba zai iya shiru kan kisan al'ummarsa ba, ya ce ya yi alkawari tsakaninsa da Allah zai kare rayukan al'ummar Borno.
Zulum ya bayyana hakan yayinda ya karɓi bakuncin gwamnonin jam'iyyar APC karkashin jagoranicn gwamnan Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu.
Gwamna Zulum ya bayyana takaicinsa kan yadda adadin masu zama a sansanin gudun hijra ke tashi, ya ce akwai bukatar mutane su koma gidajensu tun da an samu zaman lafiya a wasu guraren.
"Muna da al'umma da yawa da basu iya zuwa gonakinsu, kuma talauci ne babban ummul -aba'isin wannan ta'addancin."
Abinda muke bukata shine inda aka samu dan zaman lafiya mutane su koma gidajensu. Saboda su iya komawa sana'o'insu na rayuwa."
"Wajibi ne Sojoji su tabbatar da hakan kuma ba zan daina magana a kai ba. Ba zan gajiya ba, ba zan yi kasa a gwiwa ba kuma zan jajirce, Allah kadai ke bada mulki.
Ni ban damu da tazarce ba, idan Allah ya taimakeni na karasa wa'adin nan Alhamdu lillah."
"Amma a matsayina na gwamna in yi shiru yayinda mutane mliyan shida su mutu, ba zan ji dadi ba.
Wannan alkawari ne tsakanina da Allah cewa zan yiwa al'umma ta gaskiya. " Zulum ya fadi.
A bangare guda, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa akwai masu yiwa yaki da rikicin Boko Haram a Arewa maso gabas zagon kasa kuma ya kamata shugaban kasa ya san gaskiya.
Ina Bukatar Addu'o'in ku, Allah Yakawo Mana Karshan Wannan Wanna Matsalar. Allah Ya Bamu Zaman Lafiya
No comments:
Post a Comment