Gwamnatin tarayya ta kashe Bilyan 14 kan ciyar da dalibai, N-Power da CCT a jihar Jigawa kadai - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Sunday, August 9, 2020

Gwamnatin tarayya ta kashe Bilyan 14 kan ciyar da dalibai, N-Power da CCT a jihar Jigawa kadai

 
Gwamnatin tarayya ta kashe Bilyan 14 kan ciyar da dalibai, N-Power da CCT a jihar Jigawa kadai


Cikin kimanin shekaru 4, gwamnatin tarayya ta kashe Bilyan 14 kan shirye-shiryen ma'aikatar walwala da jin daÉ—in al'umma dake karkashin Hajiya Sadiya Umar Farouq a jihar Jigawa kadai.


Shirye-shiryen sun hada da ciyar da daliban makarantar Firamare, shirin N-Power na matasa, da shirin rabawa marasa karfi kyautan dubu biyar kowani wata.


Yayinda aka kashe N9.074bn kan shirin dubu biyar-biyar da ake ba marasa karfi a wata, an kashe Bilyan 5.178 kan shirin ciyar da daliban makarantar Firamare daga shekarar 2017 zuwa yanzu a Jigawa.


Jagoran shirin na jihar Jigawa, Bala Chamo, wanda ya bayyana hakan a hira da manema labarai a Dutse ranar Asabar ya ce an kashe bilyan N9.074 a kananan hukumomi tara, Premium Time ta dauko.


Chamo ya ce komai a shirye yake domin biyan sabbin matasan N-Power da aka dauka na sauran kananan hukumomi 18 a jihar.


Ya ce sabbin daukan su saurari jin kararrwar bankin na kudinsu daga ranar Talata, 11 ga Agusta, 2020.


A cewar Chamo, an yi amfani da kudi bilyan N9.074 ne wajen biyan albashin cikin watanni 29 ga matasa 728,367 daga farin Agusta/Satumba 2017 zuwa Maris/Afrilu 2020.


Game da ciyar da dalibai kuwa, ya ce an kashe bilyan 6 wajen samawa daliban makarantun firamarn azuzuwa 1,2, 3, 4, 5 da 6 a jihar.


Yace gwamnatin jihar na tarayya suka hada kai wajen bayar da wannan kudi.


Mr Chamo yace gwamnatin tarayya ta bada nata gudunmuwan na Bilyan N5.178 domin ciyar da daliban aji 1, 2 da 3 na tsawon kwanaki 168.


Dalibai 441,057 aka ciyar a aji 1, 2 da 3 daga Nuwamban 2017 zuwa Yulin 2019, Chamo ya kara.


Jagoran shirin na jihar yace daga baya gwamnatin jihar ta taimaki gwamnatin tarayya da kudi milyan N878 don ciyar da daliban aji na 4,5 da 6.


Ya ce dalibai434,995 aka ciyar cikin kananan hukumomin jihar 27.


No comments:

Post a Comment