Tagwayen Bama-Bamai masu ƙarfi sun jikkata sama da mutane dubu 2 Beirut
Firaministan Lebanon ya ayyana zaman makoki sakamakon mutuwar dinbin mutane a wasu tagwayen fashe-fashe masu karfi da suka auku a birnin Beirut, inda tagogin gine-gine suka tarwatse, yayin da buraguzai suka danne jama’a cikin jina-jina.
Jim kadan da aukuwar wannan iftila’in, Firaministan Lebanon, Hasan Diab ya ayyana zaman makoki, yayin da shugaban kasar, Michel Aoun ya kira taron gaggawa da majalisar tsaron kasar.
Shugaban Kungiyar Agaji ta Red Cross a Lebanon, Georges Kettaneh ya bayyana cewa sama da mutane dubu 2 da 500 ne suka jikkata, yayin da rahotanni ke cewa, akwai yiwuwar wasu sinadarai ne da jami’an tsaro suka kama a shekarun baya suka haddasa fashewar a tashar jiragen ruwan birnin na Beirut.
Shugaban rundunar tsaron kasar Abbas Ibrahim ya ce, bisa dukkan alamu, akwai gidan ajiyar karikitai da ke dauke da abubuwan fashewa da jami’an tsaro suka kwace a shekarun baya.
Hotunan bidiyo sun nuna yadda curin bakin hayaki mai kauri ke turnuke sararin samaniya, inda kuma dimbin mutane suka makale a karkashin gine-ginen da fashewar ta ruguza.
Har yanzu dai motocin daukar marasa lafiya na ci gaba da kwashe dimbin gawarwakin mutanen da suka rasa rayukansu a ibltila’in.
Tuni kasar Isra’ila ta fito ta bayyana cewa, babu hannunta a cikin wannan al’amari mai tayar da hankali.
Tuesday, August 4, 2020
New
Tagwayen Bama-Bamai masu ƙarfi sun jikkata sama da mutane dubu 2 Beirut
About Arewa Gist
SoraTemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of SoraTemplates is to provide the best quality blogger templates.
Labarai
Tags
Labarai
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment